Tinubu ya halarci daurin auren dan gwaman jihar Gombe, ya roki Gombawa su bashi kuri'iunsu a 2023

Tinubu ya halarci daurin auren dan gwaman jihar Gombe, ya roki Gombawa su bashi kuri'iunsu a 2023

  • Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC ya halarci bikin daurin auren dan gwamnan jihar Gombe a Arewa maso Gabas
  • Tinubu ya roki al'ummar Arewa maso Gabas da su bashi kuri'unsu a zaben 2023 mai zuwa, ya kuma yaba da goyon bayan da suke bashi
  • Shugaban majalisar dattawa ya marabci Tinubu, ya bayyana masa cewa, Arewa maso Gabas gida ne a gare shi

Jihar Gombe - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya dira jihar Gombe domin halartar daurin auren dan gwamna, inda ya roki Gombawa su kada masa kuri'a a 2023, rahoton Punch.

Ya kuma yabawa al'ummar yankin da irin goyon bayan da suke ba shi a aniyarsa ta gaje kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa, inda ya roki su ci gaba da tallata shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP na kada hantar Atiku, ya gana tsohon dan takarar shugaban kasan APC, Yahaya Bello

Ya bayyana rokonsa ga Gombawa ne jim kadan bayan daura auren Misbau Yahaya, dan gwamnan jihar ta Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya da Amira Babayo.

Tinubu ya halarci daurin auren dan gwamnan Gombe
Tinubu ya halarci daurin auren dan gwaman jihar Gombe, ya roki Gombawa si bashi kuri'iunsu a 2023 | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Auren da aka daura a Gombe ya samu halartar jiga-jigan siyasar Najeriya, ciki har da Boss Mustapha da ya wakilci shugaba Buhari, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba, a kwanakin baya a jihar Neja ne gwamna Yahaya ya yi alkawarin cewa, 'yan Arewa naso Gabas za su ba da kur'iunsu ga Tinubu a zaben mai zuwa.

Da yake magana, ya ce yana kyautata zaton yankin zai kawo kuri'u masu yawa tun bayan da ya zabi Shettima a matsayin abokin takararsa.

Allah ya ba da zaman lafiya

A bangare guda, ya yiwa ango da amaryarsa addu'ar zaman lafiya da rayuwar aure mai daurewa.

Da yake jawabi, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawal ya marabci Tinubu yankin Arewa maso Gabas, inda yace baya ga Kudu maso Yamma, yankin Arewa maso Gabas gida ne gareshi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Buhari Ya Ɗauki Muhimmin Mataki Na Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

A cewarsa:

"Ranka ya dade, nan ne shiyyarka ta biyu baya ga Kudu maso Yamma, nan ma shiyyarka ce ba tare da wata damuwa ba."

Gwamna Wike Na PDP Ya Gana da Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasan APC, Yahaya Bello

A wani labarin, yayin da yake ci gaba da rikici da dan takarar shugaban kasan PDP, gwamna Wike na ci gaba da kada hantar Atiku ta hanyar tarbar 'yan jam'iyyar adawa a jiharsa.

A wasu hotunan da Joe Igbokwe ta yada a Facebook ranar Juma'a 16 ga watan Satumba, an sake ganin gwamna Wike da jigon jam'iyyar APC, Alhaji Yahaya Bello.

A wannan karon, gwamna Wike ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a jiharsa ta Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel