Zulum da Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Gabas Sun Jerowa Buhari Bukatunsu

Zulum da Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Gabas Sun Jerowa Buhari Bukatunsu

  • A karshen makon nan ne duka gwamnoni na jihohin Arewa maso gabas suka yi taro a Gombe
  • Kungiyar NEGF ta koka a kan yadda yankin Arewa maso gabashin Najeriya ke da karancin lantarki
  • Wannan ya sa Gwamnonin suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta aikin wutan Mambila

Gombe - Kungiyar NEGF ta gwamnonin Arewa maso gabashin Najeriya sun yi zama na musamman, kamar yadda su kan yi duk bayan wani lokaci.

Daily Trust ta fitar da labari dazu cewa wannan kungiya tana neman gwamnatin tarayya ta hanzarta wajen aikin wutan Mambilla Hydroelectricity.

Wannan yana cikin bayanin matsayar da aka dauka yayin da gwamnonin suka yi zamansu na bakwai, an yi taro ne a gidan gwamnan jihar Gombe.

Gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sun hallara a Gombe, suka tattauna a kan abubuwan da suka shafi yankinsu.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: An kai makura, dalibai sun toshe hanyar filin jirgin sama suna zanga-zanga

Babu isasshen wuta a yankinmu - NEGF

Mai girma Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya karanta matsayar da shi da abokan aikinsa suka dauka, daga ciki an yi maganar wutar lantarki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Leadership tace gwamnonin ta bakin Mala Buni sun yi Allah-wadai da matsalar karancin wutar duk da a nan ake aikin Mambilla Hydroelectricity.

Gwamnonin Jihohin Arewa Maso Gabas
Gwamnonin jihohin Arewa maso gabas Hoto:Abdulmajid Bazza
Asali: Facebook

Gwamnonin suka ce wutar da ake warewa jihohin Arewa maso gabas bai kai 5% na karfin lantarkin Najeriya ba, duk da suke da 14% na al’ummar kasar.

Baya ga adadin mutane, NEGF tace bangarensu ke da 30% na filin da Najeriya ta mora. Duk da irin wannan albarka na yankin, ana fama da talauci sosai.

NEGF tace akwai dangantaka mai karfi tsakanin GDP da samun wutar lantarki, talauci da tsaro.

Kira ga gwamnatin tarayya

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Arewa sun fi karbar Tinubu fiye da Atiku da Kwankwaso, inji jigon APC

Kungiyar gwamnonin ta bukaci gwamnatin tarayya da Muhammadu Buhari yake jagoranta ta dage wajen ganin an yi nisa a aikin wutan Mambila a Taraba.

A karshen taron, gwamnonin jihohin sun koka a kan yadda ambaliya ke ruguza gidaje da dukiyar al’umma, aka bukaci gwamnatin tarayya ta bada agaji.

Za mu dawo tace man fetur - Minista

An samu rahoto Gwamnatin Muhammadu Buhari tana kokarin ganin ana tace gangunan danyen mai a Najeriya a maimakon a dogara da kasashen waje.

Ministan man fetur, Timipre Sylva yace an kusa karasa gyara tsohuwar matatar Fatakwal, ana kokarin ganin matatun Kaduna da Warri sun dawo aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel