2023: NNPP Tayi Fallasa a Kano, Ta Bayyana Irin Shirin da APC ke Yi a Zabuka Masu Zuwa
- Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta fallasa yadda APC ke shirin killace katinan zaben jama'ar jihar don hana su yin zabe
- NNPP ta bayyana takaicin yadda APC ta gaza bai wa rayuka da dukiyoyi kariya kuma take fatan cigaba da irin mulkin nan
- Jam'iyyar ta zargi cewa, 'dan takarar gwamna a APC ya rantse da Qur'ani kan cewa zai cogaba da barnar da ake yi a jihar ba tare da tsagaitawa ba
Kano - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi jam'iyyar APC da shirya yadda zata rage yawan masu kada kuri'u a jihar ta hanyar yaudara tare da kwace katinan zaben jama'a.
Wannan ya faru ne a karo na farko a tarihin shugabancin jihar inda aka mayar da shugabanci zuwa gado kamar yadda NNPP tace sun bayyana a dokokin gwamnatin da nade-nadenta.
Punch ta rahoto cewa, jam'iyyar ta zargi cewa, abun takaici ne da damuwa a ce "'dan takarar da gwamna ya zaba" ya rantse da Qur'ani kan cewa zai cigaba da barnar da ake a jihar Kano ba tare da dakatar da ita ba.
Jam'iyyar ta yi wannan zargin ne a takardar da ta fitar bayan taron wayar da kai da ta hadawa 'yan takarar gwamna, sanata, majalisar wakilai da majalisar jiha wanda aka yi a ranar 15 ga watan Satumban 2022 a Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Takardar ta zargi gwamnatin jihar da yin watsi da hakkokinsa na bai wa rayuka da kadarorin 'yan jihar kariya.
Kamar yadda takardar da aka saka hannu na hadin guiwa tsakanin shugaban horarwar, Garba Diso da sakatare, Hamisu Ali, sun yi kira da a hanzarta shawo kan barazanar tare da kira ga INEC da ta gaggauta wallafa sunayen wadanda basu karba katin zabe ba tare da wayar musu da kai.
An Kama Mutune 5 Kan Kisar Dan Sanata Kabiru Gaya Mai Wakiltar Kano, An Samu Karin Haske Kan Dalilin Kisarsa
A wani labari na daban, jami'an yan sandan Najeriya, reshen birnin tarayya Abuja sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu kan kisar Sadiq Gaya, dan dan majalisar Kano, Sanata Kabiru Gaya a Abuja. K
warararn majiyoyi sun tabbatar wa wakilin The Punch cewa wani abokin Sadiq ne ya kitsa yadda za a kashe shi saboda N3.5m.
Mahaifin marigayin, sanata mai wakiltan Kano ta Kudu, Gaya, dan shekara 70, sanata ne tun shekarar 2007, kuma a yanzu shine ciyaman na kwamitin INEC a majalisa.
Asali: Legit.ng