Atiku da Kwankwaso Ba Su da Karbuwa Irinta Buhari, Tinubu Na Dashi, Inji Jigon APC Keyamo

Atiku da Kwankwaso Ba Su da Karbuwa Irinta Buhari, Tinubu Na Dashi, Inji Jigon APC Keyamo

  • Yayin da ake ci gaba da tallata 'yan takarar gaje kujerar Buhari a 2023, 'yan siyasa na ci gaba da sakin zance
  • Kakakin kamfen din Tinubu ya bayyaana kwarin gwiwarsa na cewa, farin jinin Buhari zai yi tasiri ga tafiyar Tinubu
  • Sai dai, mai magana da yawun Atiku ya ce, ai kuwa dole Tinubu ya hada da gazawar Buhari a matsayin aikin dake gabansa

Najeriya - Ministan kwadago da ayyukan yi a Najeriya, Festus Kayemo, ya ce 'yan takarar PDP da NNPP; Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso kenan, ba su da wani tasiri da karbuwa a yankunan Arewacin Najeriya gabanin zaben 2023.

Wannan na zuwa bayan da mataimakiyar kakakin kamfen din Tinubu, Hannatu Musawa ta bayyana kwarin gwiwar cewa, Tinubu zai samu kuri'u a Arewa kamar yadda Buhari ya samu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa A 2023: Tinubu Na Da Karfin Da Zai Iya Farfado Da Najeriya, Yahaya Bello

Jiga-jigan na APC biyu sun bayyana wadannan maganganu ne a hira daban-daban da aka yi dasu a jiya Lahadi 18 ga watan Satumba.

Tinubu ya fi Kwankwaso da Atiku karbuwa a Arewa
Atiku da Kwankwaso ba su da karbuwa irinta Buhari, Tinubu na dashi, inji jigon APC Keyamo | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tinubu na da damar lashe zabe

Musabawa ta yi imani da cewa, dan takarar da APC ta tsayar na da dama mai karfi zaben 2023 mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta:

"Mu za mu sami kuri'un dandazon jama'a. Wannan kenan saboda za a yi zabe ne kafin Buhari ya sauka. Koma dai yaya ne, duk da cewa badi zai sauka, ba zai sauka ba har sai an yi zabe."

A bangarensa, kakakin kamfen din APC a tafiyar Tinubu, Kayemo ya bayyana cewa, kuri'u daga kungiyoyi da daidaikun mutane da dama ba na kowa bane face na Tinubu a zaben mai zuwa.

Kayemo, wanda kuma babban lauya ne ya ce, Atiku da Kwankwaso ba za su taba samun karbuwa a Najeriya irin wacce Buhari ya samu ba, WithinNigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tinubu ya je daurin auren dan gwamnan Gombe, ya roki Gombawa alfarma daya

A cewarsa:

"Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso ba su da tasiri, karbuwa da kuma kyakkyawan suna har ma da mutuncin da Buhari yake dashi a Arewa."

Da yake martani ga batun Kayemo, hadimin Atiku, Paul Ibe ya ce matukar Tinubu na son samun kuri'u irin na Buhari to dole ne ya amince tare karbar gazawar gwamnatin Buhari na shekaru bakwai.

Bayan Cikar Wa’adi, Majalisar Dattawa Za Ta Sake Duba Batun Tsige Buhari Ranar Talata

A wani labarin, wa'adin makwanni shida da aka dibarwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya warware matsalolin tsaron Najeriya sun shude, har yanzu abubuwa basu kankama ba.

A cewar rahoton jaridar The Guardian, majalisar dokokin Najeriya za ta sake zama a ranar Talata mai zuwa, 20 ga watan Satumba don sake duba batun tsige shugaban.

Idan baku manta ba, rahotanni sun karade Najeriya a ranar 27 ga watan Yuli cewa, majalisar dattawa ta dago batun tsige Buhari saboda ta'azzarar lamurran tsaro.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel