Cikakkun Sunaye: Mata 6 Cikin Yan Siyasa Da Suka Samu Shiga Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

Cikakkun Sunaye: Mata 6 Cikin Yan Siyasa Da Suka Samu Shiga Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP

  • A ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba ne jam’iyyar PDP ta saki jerin sunayen mambobin kwamitin kamfen din shugaban kasa na 2023
  • Daga cikin yan siyasa 103 da aka nada a kwamitin, mata shida ne kawai suka samu shiga
  • Wadannan yan siyasa matan sun samu shiga ne a matsayin mambobin kwamiti domin basu samu manyan mukamai ko guda ba a kwamitin

A ranar Alhamis, 15 ga watan Satumba, shugabancin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya saki jerin sunayen mambobin kwamitin kamfen din shugaban kasa na 2023.

Yan siyasar jam’iyyar 103 wadanda aka baiwa mukamai daban-daban a cikin kwanitin harda wadanda ke a matsayin mambobi.

Wasu daga cikin mambobin sun hada da Shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na PDP a 2023, Gwamna Emmanuel Udom na jihar Akwa Ibom; mataimakin shugaban kungiyar (arewa), Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da kuma mataimakin Shugaban kungiyar (kudu) Gwamna Seyi Makinde.

Kara karanta wannan

Da dumi: PDP Ta Nada Gwamnan Akwa Ibom Da Tambuwal Matsayin Shugabannin Kwamitin Kamfen Atiku

Kema Chinkwe
Cikakkun Sunaye: Mata 6 Cikin Yan Siyasa Da Suka Samu Shiga Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP Hoto: Kema Chikwe
Asali: Instagram

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, wanda ke tsare a UK sun samu shiga jerin sunayen a matsayin mambobi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, cikin manyan yan siyasar PDP 103 da suka samu shiga kwamitin yakin neman zaben, mutum shida ne kawai mata.

Wannan ya saba kiraye-kirayen da ake yi na ba karin mata damar shiga siyasa a fadin kasashen duniya.

Hakazalika, binciken Legit.ng ya kuma nuna cewa dukkanin matan da aka gani a kungiyar basu da wasu manyan mukamai da aka basu.

Za su kasance a kungiyar a matsayin mambobi kamar sauran yan siyasa 92 da sunayensu ya samu shiga.

Matan da suka shiga jerin kwamitin yakin neman zaben PDP na 2023 sune

  1. Farfesa Stella Ettah Attoe
  2. Rt Hon Margaret Icheen
  3. Sanata Stella Omu
  4. Ambasada Kema Chikwe
  5. Misis Becky Igwe
  6. Oloye Jumoke Akinjide

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya kori mai kula da shirin yafiya na shugaban kasa, ya nada wani

Zaben 2023: Ku Zabi Wadanda Suka Fara Yi Muku Aiki Suka Gaza, El-Rufai Ya Fadi Dalili

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa munanan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa kan yan ta’adda da makiyan jihar zai kare Kaduna.

El-Rufai wanda ya yi jawabi a taron kaddamar da littafin Kaduna na 4, ya jinjinawa kokarin hukumomin tsaro wajen maganin masu aikata laifuka a jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan na Kaduna ya bukaci al’ummar kasa da su zabi shugabannin da za su magance matsalolinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel