PDP Ta Nada Gwamnan Akwa Ibom Da Tambuwal Matsayin Shugabannin Kwamitin Kamfen Atiku

PDP Ta Nada Gwamnan Akwa Ibom Da Tambuwal Matsayin Shugabannin Kwamitin Kamfen Atiku

  • Daga karshe, jam'iyyar PDP ta sanar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023
  • Kwamitin na kunshe da mambobi 326 wanda ya hada da gwamnoni, tsaffin gwamnoni, dss
  • Hukumar zabe ta INEC za ta gudanar da zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan Febrairu, 2023

Jam'iyyar Adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ta nada Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal matsyain Dirakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.

Hakazalika PDP ta nada Gwamnan jihar Akwa Ibom matsayin Shugaban majalisar yakin neman zaben.

PDP a takardar da Sakataren shirye-shiryenta, Umar Bature, ya fitar ranar Alhamis, ya lissafa mutum 326 matsayin mambobin kwamitin.

A cewarsa, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, aka nada matsayin mataimakin shugaban kwamitin na Arewa yayinda Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, zai zama na kudu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo

Hakazalika an nada Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, da sauran gwamnoni matsayin mambobin kwamitin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Akwai Yiwuwar PDP Za Ta Sha Kaye A Zaben Shugaban Kasa Na 2023, In Ji Jigon PDP Mai Karfin Fada A Ji

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Cif Bode George ya gargadi jam'iyyar hamayyar cewa za ta iya shan kaye a zaben 2023 saboda rikicinta, The Nation ta rahoto.

Ya ce yadda har yanzu aka gaza warware matsalar shugabanci a jam'iyyar zai iya shafan makomarsu a zaben 2023.

George, ya yi gargadin cewa PDP tana iya rabuwa biyu Jam'iyyar PDP ta Arewa da Jam'iyyar PDP ta Kudu, idan shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, ya ki yin murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel