Buhari Ya Kori Dikio, Ya Nada Ndiomu a Matsayin Sabon Shugaban Shirin Yafiya Na Shugaban Kasa

Buhari Ya Kori Dikio, Ya Nada Ndiomu a Matsayin Sabon Shugaban Shirin Yafiya Na Shugaban Kasa

  • Shugaban kasa Manjo Muhammadu Buhari mai ritaya ya yi sabon nadi, ya kuma sallami daya daga cikin jami'in da ke rike da manyan mukamai
  • Shirin yafiya na shugaban kasa (PAP) ya samu Manjo Janar Barry Ndiomu (Mai Ritaya) a matsayin sabon shugaba bayan tsige Kanar Millan Dixon Dikio
  • A shekarar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafewa wasu tsoffin gwamnonin Najeriya da aka tsare tare da ba da umarni sakinsu

FCT, Abuja - Yanzu muke samun labarin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Barry Ndiomu (Mai Ritaya) a matsayin sabon mai kula da shirin yafiya na shugaban kasa (PAP).

Ndiomu dai zai maye gurbin tsohon mai kula da shirin ne Kanar Millan Dixon Dikio (mai ritaya) bisa umarnin Buhari, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Baiwa Yan Wasan Gudu Kyautar N200m Da Lambar Yabo

Buhari ya nada sabon shugaban shirin yafiya na shugaban kasa
Buhari Ya Kori Dikio, Ya Nada Ndiomu a Matsayin Sabon Shugaban Shirin Yafiya Na Shugaban Kasa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wata sanarwa hadimin Buhari, Femi Adesina ya fitar ta ce:

“Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada Manjo Janar Barry Tariye Ndiomu (mai ritaya) a matsayin shugaban rikon kwarya na shirin yafiya na shugaban kasa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kadan daga tarihin Ndiomu

Rahoton da muka samo ya ce, Odoni dake karamar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa, kuma ya yi karatu a makarantar horas da sojoji ta NDA.

Ya kai matsyain laftana a 1983 sannan ya yi ritaya daga aikin soja a shekarar 2017, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakazalika, jami'in horarren lauya ne kuma tsohon dalibi ne a wasu manyan makarantu a duniya ciki har da Harvard Kennedy School.

Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

A wani labarin, majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

Asali: Legit.ng

Online view pixel