Rikici ya kunno: An Zargi Shugaban Matasa da Fifita Yarbawa a Taron Jam’iyyar APC

Rikici ya kunno: An Zargi Shugaban Matasa da Fifita Yarbawa a Taron Jam’iyyar APC

  • Jam’iyyar APC mai mulki za tayi wani babban taro da zai tara matasan Najeriya da ke da akidar ta
  • Kafin ayi nisa a shirye-shiryen taron, an fara kukan cewa Dayo Isreal bai tafiya da matasan Arewa
  • Shugaban matasan APC a Najeriya, Isreal yayi magana a shafukansa, ya karyata zargin da ake yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban matasan APC na kasa, Dayo Isreal ya samu sabani da mataimakinsa Jamaldeen Kabir game da wani taron matasa da ake shirin yi.

The Cable tace matsalar ta fito fili ne yayin da aka fitar da jerin sunayen ‘yan kwamitin shirya taron matasan jam’iyyar APC da za ayi a watan Satumban nan.

Jamaldeen Kabir ya fito shafinsa na Facebook yana cewa bai da labarin wannan taro da ake shirin yi a Abuja, yace sam babu hannunsa a duk wasu shirye-shirye.

Kara karanta wannan

‘Dan takara Ya Ba Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

Mataimakin shugaban APC na kasan ya fadakar da magoya bayan jam’iyya da ke jihohi 19 na Arewa da birnin tarayya cewa ba da shi aka tsara taron nan ba.

Amma tuni shugaban na sa ya maida martani a shafinsa, yana nuna Kabeer ya san da maganar, kuma har ya turo hoton da za ayi masa amfani da shi a taron.

Kwamitin yarbawa ko matasan APC?

Isreal ya wanke kan shi, yace zargin da ake yi masa na cika kwamitocin da Yarbawa ba gaskiya ba ne. A karshe ya tabbatar da za ayi taron a karshen makon nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Taron Jam’iyya
Matasa a wajen taro a Najeriya Hoto: @dayoisrael
Asali: Twitter

Matashin yace a kwamitin yada labarai mai mutum 37, akwai ‘Yan Arewa 21. A kwamitin kudi da aka sa mutane 43, mutum 19 daga Arewacin Najeriya suka fito.

Sannan akwai 'Yan Arewa tara a kwamitin da zai tantance wadanda za su halarci taron.

Kara karanta wannan

A Raba Aurenmu Don Baya Aikin Komai Sai Jajibe-jajiben Fada, Matar Aure Ta Roki Kotu

Ba ayi damu inji masu korafi

A jawabin da ya yi a shafinsa, Israel ya nuna yadda yake kokarin tafiya da kowa. Amma wasu matasan sun zarge shi da goge wata magana da ya yi Twitter.

Da wani matashi mai goyon bayan APC da Bola Tinubu yake bayani, yace an kawo sunan irinsu Hon. Sha'aban Ibrahim Sharada wanda yanzu ya bar jam’iyya.

Wani kuma ya yabi tsohon shugaban matasan APC na kasa, Ismaeel Ahmed, yace a lokacinsa an tafi da kowa, amma yanzu ana nunawa wasu bambanci a APC.

FFK ya ragargadi Obi

Dazu aka ji labari Femi Fani-Kayode yace Peter Obi ya sani sarai ba zai ci zabe ba, shiyasa yake neman tada yaki tsakanin Hausawa, Yarbawa da Ibo a Najeriya.

Jigon na APC ya tona wadanda suke tare da ‘Dan takaran shugabar kasar, yace babu jihar da jam’iyyar LP za ta iya samun 10% a 2023 duk da hayaniyar da ake ta yi.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Sharbi Kuka Da Hawaye Bayan Ya Gano Cewa An Yi Baikon Budurwarsa Da Wani

Asali: Legit.ng

Online view pixel