‘Dan takara Ya Fadawa Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

‘Dan takara Ya Fadawa Gwamnati Satar Amsar Magance Matsalar ASUU a Kwana 30

  • Peter Obi yana ganin gwamnatin Muhammadu Buhari za ta iya biyan bukatun da ASUU suka zo da shi
  • ‘Dan takarar shugaban kasar yace idan aka yi amfani da cinikin danyen man wata daya, an gama magana
  • Tsohon gwamnan ya zargi gwamnati da kin maida hankali domin ganin dalibai sun koma karatu jami’o’i

Abuja - Peter Obi mai takarar shugabancin Najeriya a inuwar Labour Party ya sake yin magana a game da yajin-aikin da ‘Yan ASUU suke yi.

Malaman jami’a sun shafe wata da watanni suna yajin-aiki a Najeriya, Channels TV ta rahoto Peter Obi yana cewa za a iya kawo karshen lamarin.

Peter Obi yace gwamnatin tarayya za ta iya biyan bukatun kungiyar malaman jami’a idan aka yi amfani da kudin da ake samu daga danyan mai.

Kara karanta wannan

Masoya Sun Rude da Jin Rade-radin Kai wa ‘Dan takarar Shugaban Kasa Hari

‘Dan takaran ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta niyyar magance wannan matsala ne, amma yace Najeriya tana da kudin da ake nema.

An yi gangami a Abuja

Obi ya yi wannan jawabi a wajen wani taro na musamman da aka shirya jiya a garin Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shawarar da Obi ya bada ita ce a karkatar da duk dukiyar da aka samu daga cinikin danyen man fetur da wata daya rak, domin a koma karatu.

‘Dan takaran LP
‘Dan takaran LP, Peter Obi Hoto: @NaijaWeCan
Asali: Twitter

NLC tana tare da Obi

An rahoto cewa Femi Falana ya yi jawabi a wajen taron, ya zargi gwamnati da kin hukunta wadanda suke sace danyen man da ake da shi.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa, Ayuba Wabba ya bayyana cewa za su umarci ‘yan kungiyar NLC da ke fadin Najeriya su zabi Obi a 2023.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya Ya Sace Naira Biliyan 4 - ICPC

ASUU: Watanni 7 da rufe jami'o'i

Ba wannan ne karon farko da ‘dan takaran ya tofa albarkacinsa a game da wannan dogon yajin-aikin jami'o'i da ya ki ci, kuma ya ki cinyewa ba.

Kwanaki Legit.ng Hausa ta fahimci ya koka a kan yadda hukumar TETFund take facaka da kudin da ake warewa domin kula da jami’o’in kasar.

Da yake magana a shafin Twitter, Obi yace hukumar ba ta sauke nauyin da aka daura mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel