Mayaudari ne: Fani-Kayode Ya Ankarar da ‘Yan Najeriya, Ya Bayyana Wanene Peter Obi

Mayaudari ne: Fani-Kayode Ya Ankarar da ‘Yan Najeriya, Ya Bayyana Wanene Peter Obi

  • Femi Fani-Kayode ya kira ‘Dan takaran LP, Peter Obi da makaryaci, mara gaskiya kuma mayaudari
  • Kwanaki Peter Obi ya zargi magoya bayan Bola Tinubu da kiran Yarbawa da su guji zaben shi a 2023
  • Fani-Kayode yace wannan aikin na kusa da 'Dan takaran ne ba magoya bayan ‘dan takaran APC ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Femi Fani-Kayode ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai hadari, mayaudari kuma mara gaskiya.

Tsohon Ministan harkokin jiragen saman ya yi wannan bayani a duka shafukansa na sada zumunta a ranar Litinin, a matsayin raddi ga Peter Obi.

Femi Fani-Kayode yake cewa ‘dan takaran na jam’iyyar LP yana kokarin hada rigima tsakanin mutanen Kudu maso yamma da na kudu maso yamma.

Abin ta kai ‘dan siyasar ya yi kira ga manyan yankin kudu maso gabas su ja kunnen Peter Obi. Tsohon jigon na PDP yana goyon bayan Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Karyar Peter Obi Ta Wadatar Da Afirka Baki Daya', Fitaccen Jigon PDP Ya Ragargaji Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP

Vanguard ta rahoto cewa Fani-Kayode ya fara maganarsa da kiran ‘dan takaran makaryaci.

Peter Obi Grassroots Mobilization
Peter Obi Hoto: @PO_GrassRoots
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kai MAKARYACI ne

“Peter, kai ba kowa ba ne illa MAKARYACI.”
“Sunan wanda ya yada sakon WhatsApp da ka tallata a bidiyonka, wanda na wallafa shi a nan, wani mutum ne Powell Glad Legbe...
Wanda Inyamuri ne, kuma mai nuna kiyayya ga sauran kabilu, wanda ya tsani Yarbawa, Hausawa, Fulani, da Ijaw, kuma yana kusa da kai.”
Shiyasa ka boye sunan shi, ka ki bayyanawa Duniya a bidiyon na ka."

FFK yake cewa wannan sako ba daga kungiyar Tinubu Support Group ko Yarbawa ya fito ba. A dalilin haka yace Obi mayaudari ne wanda yake da hadari.

Ba zai ci zabe ba, yana neman hada fada

Bugu da kari, an rahoto Fani-Kayode yana cewa ‘dan takaran shugaban kasar na neman hada yaki tsakanin Hausawa, Yarbawa da Ibon da ke Najeriya.

Kara karanta wannan

Masoya Sun Rude da Jin Rade-radin Kai wa ‘Dan takarar Shugaban Kasa Hari

A cewar Fani-Kayode, LP ba za ta samu ko 10% a kowace jihar kasar nan a 2023 ba, ya zarge shi da neman cin ma burinsa na shiga Aso Villa da sunan Ibo.

Bayanin da ‘dan siyasar ya yi a shafinsa ya kara da cewa wadanda suka zagaye Peter Obi ba mutanen kwarai ba ne, miyagu ne da za su kai shi ga halaka.

Muna yin ka - NLC ga Obi

A baya an ji labari shugaban kungiyar ‘yan kwadagon Najeriya, Ayuba Wabba ya bayyana cewa ma’aikatan Najeriya za su zabi Peter Obi a zaben 2023.

Zuwa yanzu an yi watanni bakwai da rufe jami'o'in gwamnati, Peter Obi yana ganin ba gwamnatin tarayya ba tayi niyyar sasantawa da 'Yan ASUU ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel