Sai da lissafi: Mutanen Peter Obi Sun Shirya Dabarar Doke Atiku, Kwankwaso da Tinubu

Sai da lissafi: Mutanen Peter Obi Sun Shirya Dabarar Doke Atiku, Kwankwaso da Tinubu

  • Kungiyar Peter Obi Support Group za ta maida hankali a kan wasu jihohi a zaben shugabancin kasa
  • Shugaban POPSG a Duniya, Felix Obaze yace akwai tsokar kuri’u a Abuja, Legas, Ribas Kano da Kaduna
  • Felix Obaze yace idan Peter Obi ya iya lashe kuri’un wadannan jihohi, LP za ta doke sauran jam’iyyu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kungiyar Peter Obi Support Group (POPSG) ta magoya bayan Peter Obi sun fara shirye-shiryen zaben shugaban kasa da za ayi a farkon 2023.

This Day ta rahoto kungiyar POPSG tana cewa akwai jihohi biyar da Peter Obi yake bukatar ya yi galaba a zaben badi domin ya zama shugaban Najeriya.

Shugaban wannan tafiya, Felix Obaze ya yi wannan bayani wajen kaddamar da shugabannin kungiyar na reshen Abuja da aka yi a karshen makon jiya.

Kara karanta wannan

Cikin Okowa Ya Duri Ruwa, Ya Fadi ‘Dan Takara 1 da Zai Kawo Masu Cikas a 2023

Obaze yake cewa za su maida hankali wajen yin nasara a jihohi biyar da kuma birnin tarayya.

Su wane jihohi ake magana?

Jihohin da magoya bayan na Peter Obi suke hari su ne Legas, Ribas Kano, Kaduna, da Nasarawa. Kusan dukkaninsu su na yankin Arewacin Najeriya ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Obaze, tulin kuri’un da za a kada a zaben shugaban kasa za su fito daga nan ne. Duk da haka, kungiyar POPSG za ta dage wajen lashe wasu jihohin.

Mutanen Peter Obi
Peter Obi a wajen taron siyasa Hoto: @PO_GrassRoots
Asali: Twitter

Shugaban 'yan Peter Obi Support Group yake cewa idan ‘dan takaran na Labor Party ya samu nasara a wasu karin jihohi, babu shakka za su kai labari a 2023.

Akwai alamun nasara - POPSG

“Muna da jihohi 36 a Najeriya da birnin tarayya Abuja, akwai kuma jihohin da muke dauka da muhimmanci saboda adadin masu zabe a jihohin.

Kara karanta wannan

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

Jihohi irinsu Legas, Ribas, Kano, Kaduna, Nasarawa, da Abuja su ne gaba a yawan masu kuri’a.”

- Felix Obaze

Ana sa ran rantsar da shugabannin wannan kungiya na reshen garin Abuja zai taimakawa Obi wajen doke jam’iyyu irinsu APC, PDP da NNPP a badi.

“Shugabannin kungiya na reshen Abuja za su jawo mana dubban ‘yan Najeriya daga lungunan Abuja a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.”
“Kungiyar tana da rassa a jihohi 36 da ke Najeriya da Abuja, da kuma kasashen kasar waje.”

- Felix Obaze

LP za ta samu kuri'u - Umahi

Kwanaki kun ji labari Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi yana ganin cewa ‘dan takaran LP zai tashi da kuri’u rututu a yankin Kudu maso gabas.

Dave Umahi yace kuri’un da Obi zai samu ba za su sa ya doke APC ba, amma takararsa na da amfani wajen ganin Ibo ya karbi mulki nan gaba.

Kara karanta wannan

Likitoci 38, 000 Sun Bi Bayan Peter Obi, Sun Sha Alwashin Kawo Masa Kuri’u Miliyan 25

Asali: Legit.ng

Online view pixel