Gwamnan APC Ya Bayyana Illar da Obi Zai Yi Masu, Ya Ayyana Magajin Buhari

Gwamnan APC Ya Bayyana Illar da Obi Zai Yi Masu, Ya Ayyana Magajin Buhari

  • David Umahi ya ziyarci Muhammadu Buhari, ya yi magana a game da damar Peter Obi a zaben 2023
  • Gwamnan na jihar Ebonyi yana ganin ‘dan takaran LP zai tashi da kuri’u rututu a yankin Kudu maso gabas
  • Umahi yace kuri’un da Obi zai samu ba zai sa ya doke APC ba, amma yace takararsa tana da amfani

Abuja - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi yace Peter Obi zai samu tarin kuri’u a zaben shugabancin kasa daga kudu maso gabashin Najeriya.

The Cable tace David Umahi ya zanta da ‘yan jarida bayan ya yi zama da Mai girma shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a a fadar Aso Villa.

Gwamnan yake cewa ‘dan takaran jam’iyyar LP watau Peter Obi zai samu kuri’u da-dama a yankin Ibo, amma hakan ba zai sa ya zama shugaba ba.

Kara karanta wannan

2023: Ana Gabanin Fara Kamfe, Kwankwaso Ya Ja-kunnen Tinubu, Atiku da Peter Obi

Duk da farin jinin da tsohon gwamnan na Anambra da jam’iyyarsa take yi, Gwamna Umahi ya fadawa ‘yan jarida hakan bai nufin LP za ta doke APC.

“Yayin da jam’iyyata ta samu nasara, shi kuma ya yi tanadi da kyau domin kudu maso gabas su fito da shugaban kasa, ka da wani ya raina mu.
Kuma za ku iya ganin irin karbuwar da ya yi, wanda wannan bai nufin zai samu galaba a kan jam’iyyar APC. Ina mai tabbatar da wannan.”

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- David Umahi

Gwamnan APC
Gwamna David Umahi Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Tafiya ce mai kyau

“Ta tabbatar da mutanen Kudu maso gabashin kasar nan sun samu karbuwa; mun san wata rana za muyi mulki, wannan na da muhimmanci.
An kafa tafiyar Peter Obi ne kan adalci da gaskiya. Ba zai kai ga nasara nan-take ba, domin dole in kare jam’iyyata; dole in goyi bayan jam’iyyata.

Kara karanta wannan

Rade-radin Rigima: Bola Tinubu Ya Yi Bayani Kan Alakarsa da Shugaban APC na Kasa

Dole in yi fatan alheri ga jam’iyyata, ina takara a jam’iyyar. Ko abin da yake yi yana da ma’ana ko babu, a Kudu maso gabas, yana da ma’ana.”

Abin da ya sa Tinubu zai ci zabe

Sun ta rahoto Umahi yana cewa Bola Tinubu zai yi galaba saboda APC tayi karfi a fadin kasar nan, kuma za a sasanta duk wani rikicin gida.

“Mai girma shugaban kasa, ‘dan takarata da mataimakinsa da shugaban jam’iyya sun dauki matakan da za a bi domin dinke barakar da ake da su."

- David Umahi

Kiran Kwankwaso ga 'Yan takara

A yayin da ya kai ziyara zuwa Adamawa inda ya kaddamar da ofishin jam’iyyar NNPP, an ji labari Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga masu takara.

Wasu suna kukan cewa ya kamata a takawa tsohon Ministan tsaro burki domin ya fara yin kamfe alhali ba a shiga kakar yakin neman zabe ba tukuna.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: Jonathan Ya Jefa Mu Halin da Ake Ciki a Yau Inji Ministan ilmi

Asali: Legit.ng

Online view pixel