Gwamna Buni Zai Maye Gurbin Marigayi Kwamishinansa da Dansa

Gwamna Buni Zai Maye Gurbin Marigayi Kwamishinansa da Dansa

  • Ana ta shirye-shiryen yadda za a maye gurbin kwamishina matasa da wasanni na jihar Yobe da rasu a watan jiya
  • Majiyoyi sun shaida cewa, ana kyautata zaton gwamna Buni zai dauko dan tsohon kwamishinan domin zama a kujerarsa
  • Sai dai, wasu na kusa da marigayin an ce suna kulla yadda hakan ba zai faru saboda wasu dalilai nasu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Yobe - Kwanaki kasa da 40 bayan rasuwar tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar Yobe, Goni Bukar Lawan, ‘yan siyasan jihar na kai kawo don ganin an maye gurbinsa.

The Nation ta tattaro cewa, da yawan 'yan siyasa daga karamar hukumar su marigayi kwmaishina sun amince a nada babban dansa, Kachalla Goni Bukar a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Sai dai kuma wasu makusanta kuma abokan marigayi kwamishinan ba sa goyon bayan wannan tsari na dauko dansa.

Kara karanta wannan

ASUU: An kai makura, gwamnatin Buhari ta yi sabon batu, ta fadi kokarinta a dinke matsalar ASUU

Mai Mala Buni zai maye gurbin kwamishina da dansa
Gwamna Buni zai maye gurbin marigayi kwamishinansa da dansa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wata majiya ta kusa da Gwamna Mai Mala Buni ta shaida cewa, gwamnan zai nada Kachalla, babban dan tsohon kwamishina domin ya maye gurbin mahaifinsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar majiyar:

“Ina da masaniyar cewa gwamnan na jiran a kammala zaman arba'in ne kafin ya bayyana wanda zai maye gurbin karamar hukumar ta Bursari da BUGON a majalisar zartarwa ta jiha."

Hakazalika, jaridar ta samo daga tushe cewa, akwai masu kokarin ba a ba dan marigayi kwmaishina kujerar ba saboda a ganinsu ya yi kankanta da rike mukamin.

Kachalla, wanda shi ma ma'aikacin gwamnati ne a jihar ta Yobe an haife shi a shekarar 1992, dalilin da yasa wasu ke ganin ya yi kankanta.

Idan baku manta ba, Allah ya yiwa kwamihsina Goni Bukar Lawan rasuwa a ranar 2 ga watan Agustan da ta gabata, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

Gwamna Buni Ya Yi Wa 'Ya'yan Sheikh Goni Aisami Wata Babban Alfarma

A wani labarin, gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya umurci a bawa yayan malamin addinin musulunci da aka kashe, Sheikh Goni Aisami, a ranar Juma'a aiki kai tsaye, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Buni ya bada umurnin ne a lokacin da iyalan malami da aka hallaka suka ziyarci shi don nuna godiyarsu bisa damuwar da ya nuna kan lamarin.

Buni ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta yi bincike kan yadda aka yi malamin ya rasu. Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnati za ta cigaba da tallafawa iyalan duba da cewa sun rasa mai kula da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.