Mun Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin Mun Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU, Gwamnatin Buhari

Mun Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin Mun Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU, Gwamnatin Buhari

  • Ministan ilimi a Najeriya ya ce gwamnatin Najeriya ta yi iyakar kokarinta wajen shawo kan matsalar ASUU
  • Kungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta shafe sama da watanni shida tana yaji, lamarin da yasa dalibai ke zaune a gida
  • Wasu jami'o'in Najeriya sun baude wa yajin na ASUU, sun nemi ma'aikata da dalibai su dawo makaranta

FCT, Abuja - Bayan da aka shafe watanni ana kai ruwa rana a batun yajin aikin ASUU, gwamnatin Buhari a ranar Talata ta ce ta yi iyakar kokarinta don ganin ta kawo karshen rikicin gwamnati da kungiyar malaman jami'o'i.

Wannan na fitowa ne daga bakin ministan ilimi, Adamu Adamu a wata ganawa da ake yi da shugabannin jami’o’in tarayya da hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a Abuja.

Kara karanta wannan

Pantami: Yadda Na Shawo Kan Buhari, Aka Fasa Kara Farashin Yin Waya da Sayen Data

Gwamnatin Buhari ta ce ta iya kokarinta a yajin ASUU
Mun Yi Duk Mai Yiwuwa Don Ganin Mun Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU, Gwamnatin Buhari | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya zuwa yanzu dai da rahoton nan ke shigowa mana daga jaridar The Nation, an ce manyan jami'an na gwamnati suna cikin ganawar sirri.

Ana sa ran minista Adamu zai yi wa manema labarai bayani da zarar an kammala ganawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista Adamu ya batu daga shugaba Buhari na kan matsayar cewa, duk da ana kokarin malamai su koma bakin aiki, amma ba za a maimaita kuskuren rubuta wata yarjejeniya da ba za ta haifar da da mai ido ba.

A cewarsa:

"Mun yi iyakar kokarinmu a irin wannan yanayin. Bayan shawari da juna tsakanin ma'aikatu da doguwar tattaunawa mai zurfi da dukkan hukumomin gwamnati, mun yi tattauna da kungiyoyin kwadago."

Ni da kaina na yi kokari, amma abin ya ci tura, inji minista Adamu

Ya kuma bayyana cewa, shi kansa ya yi duk mai yiwuwa tare da jan kungiyoyin a jiki da duk wasu bayanan da suka dace amma abin ya ci tura, rahoton DailyPost.

Kara karanta wannan

Tura ta kaI bango: Daliban Najeriya sun gaji da yajin ASUU, sun tura wani sako ga Buhari

Ya kara dacewa:

“Misali na gana da shugabannin kungiyar ta ASUU kai tsaye a gidana da ofishina har ma a sakateriyar ASUU a lokuta mabambanta, baya ga sauran maganganu da ake ci gaba da yi."
"Magana ta gaskiya game da dukkan kungiyoyin nan, musamman ASUU, babban batun da aka gaza warwre tsakanin gwamnati da kungiyoyin shine batun dokar "Babu Aiki, Babu albashi".
“Magana ta gaskiya, gwamnati ta fadi karara cewa ba za ta karya dokar ba."

A bangare guda, ya godewa kungiyoyin da suka fahimci matsayar gwamnati na dokar babu aiki babu albashi.

Bayan Kiran Dalibai, Jami’ar Gombe Ta Yi Watsi da ASUU, Ta Kira Malamai Su Dawo Aiki

A wani labarin, hukumar gudanarwar jami'ar jihar Gombe (GSU) ta kira dukkan malaman ta bukaci dukkam ma'aikatanta dake hutun karatu da su gaggauta dawowa aiki.

Wannan na zuwa kira na zuwa ne a yau Litinin 5 ga watan Satumba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'ar Arewa ta yi watsi da ASUU, ta ce malamai su gaggauta dawowa bakin aiki

Magatakardar jami’ar, Dakta Abubakar Aliyu Bafeto, a cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan Satumba 5, 2022, ya umurci malaman jami'ar da ke karatu a Najeriya da su koma bakin aiki kasancewar jami'ar ta dawo karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel