Gwamna Buni Ya Yi Wa 'Ya'yan Sheikh Goni Aisami Wata Babban Alfarma

Gwamna Buni Ya Yi Wa 'Ya'yan Sheikh Goni Aisami Wata Babban Alfarma

  • Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bawa yayan marigayi Sheikh Goni Aisami da aka kashe, su biyu guraben aiki kai tsaye
  • Buni ya sanar da hakan ne yayin da iyalan shaihin malamin suka kai masa ziyara a gidan gwamnati saboda nuna damuwarsa kan rasuwar mahaifinsu
  • Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi jawabin godiya a madadin iyalan shaihin ya ce guraben aikin da aka bawa yayan zai taimaka wurin rage musu wahalhalu duba da mai kula da su ya rasu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya umurci a bawa yayan malamin addinin musulunci da aka kashe, Sheikh Goni Aisami, a ranar Juma'a aiki kai tsaye, Daily Trust ta rahoto.

Gwamna Buni ya bada umurnin ne a lokacin da iyalan malami da aka hallaka suka ziyarci shi don nuna godiyarsu bisa damuwar da ya nuna kan lamarin.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Yace Zai Iya Tuka Mota daga Abuja Zuwa Kaduna Ba Jami'an Tsaron Lafiyarsa

Aisami da Buni
Gwamna Buni Ya Yi Wa 'Ya'yan Sheikh Goni Aisami Wata Babban Alfarma. Hoto: Independent NG.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buni ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta yi bincike kan yadda aka yi malamin ya rasu.

Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnati za ta cigaba da tallafawa iyalan duba da cewa sun rasa mai kula da su.

Iyalan Aisami sun yi wa gwamna godiya

Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi magana a madadin iyalan, ya yi godiya bisa tawagar da gwamnan ya tura gidan marigayin don yin gaisuwan mutuwa, Independent ta rahoto.

Ya ce guraban aikin da aka bada zai taimaka wurin rage wa iyalan wahalhalun da za su fuskanta bayan rasuwar malamin.

Rahotanni sun ce wasu sojoji biyu ne suka kashe Sheikh Aisami a ranar Juma'a da ta gabata.

Yan sanda sun kama wadanda ake zargin sannan Rundunar Sojoji ta sanar da nata binciken tana mai cewa duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Na Bar Koyarwa Har Abada Idan Aka Hana Mu Albashin Watanni 6 Inji Malamin Jami’a

An Kama Sojoji 2 Kan Laifin Kashe Babban Malamin Islama, Sheikh Goni Aisami, Tare Da Sace Motarsa A Yobe

Tunda farko, kun ji cewa Rundunar yan sandan Najeriya a Yobe ta kama sojoji da ake zargi da hannu a kisar fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami wanda aka kashe ranar Juma'a misalin ƙarfe 9 na dare a hanyarsa ta komawa Gashua daga Kano.

Majiyoyi da dama daga garin sunyi zargin cewa sojojin sun kashe malamin ne bayan ya rage musu hanya daga shingen sojoji a Nguru zuwa Jaji-maji, wani gari da ke karamar hukumar Karasuwa na Jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel