Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

  • Gwamna Nyesom WIke na jihar Ribas ya sha alawashin lallasa tare da mitsike makiyansa na siyasa a Najeriya
  • Ya bayyana cewa, ba zai bar ubangiji ya yi maganin makiyansa ba, da kansa zai tabbatar da ya ga bayansu
  • Tuni dai rikicin cikin gida yake cigaba da kamari a jam'iyyar APC inda Wike da tawagarsa ke ta hankoron saukar Iyorchia Ayu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abia - Ana tsaka da rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a ranar Litinin yace ba zai bar makiyansa a siyasa Ubangiji ya yi maganinsu ba, da kan shi zai lallasa su kuma ya mitsike su inda ya kwatanta su da kananan yara.

Nyesom Wike
Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike. Hoto daga channelstv.com
Asali: Twitter
“Ubangiji ya bani damar mitsike wadannan mutanen, ya bani damar ganin bayan makiyana,”

Channels TV ta rahoto cewa, Wike yace a Aba dake jihar Abia lokacin da yaje kaddamar da wasu titina.

Wike wanda takwaransa na jihar Abia, Gwamna Okezie Ikpeazu, ya karba bakunci, yace ya fahimci alaka inda ya kara da cewa babu wanda zai iya karya matsayinsa a wurin ‘yan uwansa na PDP da abokansa kamar su Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin kwanakin nan, Wike da mukarrabansa an gan su tare a kasar waje kuma sun dauka matsaya daya ta bukatar shugaban PDP na kasa Iyorchia Ayu da yayi murabus ya bar wa ‘dan kudu kujerarsa.

“Babu alaka da ake iya siya da kudi. Idan ina karanta jaridu, suna cewa wasu mutane na kokarin karya matsayinsu. Nace kun gane manufar abinda muke yi? Idan sun fahimta, ba za su bata lokaci ba.
“Idan kun so ku je ku samu Ikpeazu, idan kun so ku je kusamu Seyi, idan kun so ku je ku samu Ugwuanyi. Ba ma ku san abinda ku ke yi ba… kuma kuskure ne.”

- Gwamnan Ribas yace.

Wike ya kara da cewa, Ayu ya mutunta yarjejeniya tare da murabus ko kuma ‘yan Najeriya za su san wanda ke da muhimmanci ko rashinsa idan lokaci yayi.

Yadda Tinubu da Tawagar Wike Ke Shirya Yarjejeniyar Nasara a Zaben 2023

A wani labari na daban, akasin yadda ake ta hasashe kan cewa tsagin Gwamna Wike na jam'iyyar PDP zasu koma APC bayan ganawarsu da 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, Bola Tinubu, an gano cewa aiki suke tare don ganin nasarar APC a zaben shugaban kasa, Vanguard ta tabbatar da hakan.

Dukkan bangarorin biyu sun gana a UK wanda ya janyo aka dinga hasashen cewa gwamnonin PDP da suka hada da Seyi Makinde, Samuel Ortom, Okezie Ikpeazu tare da Nyesom Wike suna shirin sauya sheka ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel