Babu Ruwan Coci da Siyasar Jam’iyya, Shugaban CAN Ya Caccaki Wasu Fastoci

Babu Ruwan Coci da Siyasar Jam’iyya, Shugaban CAN Ya Caccaki Wasu Fastoci

  • Shugaban kungiyar CAN ya bayyana cewa, bai kamata coci da sauran wuraren addini su zama masu tallata jam'iyya ba
  • Tun bayan zaben Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a APC ake ta cece-kuce a kai
  • Ba sabon abu bane a Najeriya a samu kungiyar addini na tallata dan takara ko wata jam'iyya gabanin zabe

Onitsha, jihar Anambra - Shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN), Dr Daniel Okoh, ya shaewarci shugabannin kiristoci a fadin Najeriya da su kauracewa batutuwan da suka shafi siyasa.

Ya kuma shawarci ‘yan Najeriya da su yi karatun ta natsu wajen zaben shugabannin da za su mulke su a nan gaba, rahoton Punch.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a garin Onitsha, ranar Lahadi 4 ga watan Satumba a bikin maulidin shekaru 75 na mu'assasin kungiyar Grace of God Mission International, Bishop Paul Nwachukwu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Coci ba rumfar tallan dan takara bane, inji shugaban CAN
Babu ruwan Coci da siyasar jam'iyya, inji shugaban kungiyar CAN | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Okoh ya kuma bayyana cewa, zaben na 2023 ne zai ba masu kada kuri'u damar daura shugabannin da suke so ta hanyar zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce ya yi imanin cewa, cocin na da matukar tasiri wajen kawo shugaban Najeriya na gaba zaben na 2023 mai zuwa, haka nan kafar Labarai ta Kemi Filani ta tattaro.

A kalamansa:

“Kamata ya yi a ce babu ruwan coci da batun jam'iyya, coci na da alhakin tabbatar da nunawa jama'a abin da ya dace wajen zaben shugabannin da ya kamata su zaba. Idan ’yan Najeriya za su hada kai waje guda, to za su iya juya kasar nan da hannayensu."

Da yake jawabi karin haske, babban fasto na Destiny Revival Ministry International, Godwin Okeke, ya yi ruwan kalamai masu zafi ga sauran fastoci masu tallata ’yan siyasa a cocunansu.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Bayyana 'Yan Takara Da Ya Kamata Matasan Najeriya Su Zaba

Ya bayyana cewa, irin wadannan dabi'u na kawo tasgaro da cikas ga tafiyar da al'amaru a cikin kasar.

Okeke ya ce kamata ya yi a ce coci ya koma gefe da batun jam'iyya, amma dai ya fadakar, ya wayar da kan jama’ar kan harkokin zabe.

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta ki amincewa da zabo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Da yake magana a wata hira da jaridar Punch a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, mai magana da yawun CAN, Adebayo Oladeji, ya ce yanke irin wannan shawari a cikin kasa mai cike da rudani irin Najeriya, mataki ne da bai dace ba.

Ya bayyana cewa, kasar na da fasto a matsayin mataimakin shugaban kasar kuma ake kashe malamai da mabiya addinin kirista, to lallai babu tabbacin kiristoci za su samu aminci a mulkin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

Manyan 'Yan Siyasa 10 Masu Karfin Tasiri a Zabukan 2023 Dake Gabatowa

Asali: Legit.ng

Online view pixel