Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

  • Zaben Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Bola Tinubu na ci gaba da jawo martani daban-daban a fadin kasar nan
  • Kungiyar kiristocin Najeriya ta ce matakin da Tinubu ya dauka na zabo dan uwansa musulmi mataki ne da bai dace ba
  • Kungiyar ta kiristoci ta kara da cewa da irin wannan shawarar, babu tabbas kiristoci za su kasance cikin aminci a kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya - Kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta ki amincewa da zabo tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Da yake magana a wata hira da jaridar Punch a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, mai magana da yawun CAN, Adebayo Oladeji, ya ce yanke irin wannan shawari a cikin kasa mai cike da rudani irin Najeriya, mataki ne da bai dace ba.

Kara karanta wannan

Atiku: Sai da APC da su Buhari suka dawo da Najeriya baya cikin shekaru 7 kacal

Martanin CAN game da zabo musulmi ya yi takara da Tinubu
Tinubu da Shettima a 2023: CAN ta yi martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi | Hoto: barristerng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, kasar na da fasto a matsayin mataimakin shugaban kasar kuma ake kashe malamai da mabiya addinin kirista, to lallai babu tabbacin kiristoci za su samu aminci a mulkin Musulmi da Musulmi.

Oladeji, ya yi gargadin cewa ‘yan Najeriya su kasance a shirye su fuskanci girbar abin da shuka idan suka amince da tikitin Musulmi da Musulmi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalamansa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito:

“Mun san wannan shi ne abin da zai yi kuma mun yi gargadi a kan hakan. Ya rage ga ‘yan Najeriya su yanke shawarar abin da suke so.
“Dukkan ku kuna raye lokacin da muka gargadi Buhari da kada ya bari Musulmi su mamaye tsarin tsaron kasar nan kuma ya yi hakan. Ina tsammanin za mu iya ganin yadda 'yan ta'adda ke aiki cikin alfahari.

Kara karanta wannan

Tinubu: Abin Da Yasa Na Zabi Musulmi A Matsayin Abokin Takara Na A 2023

"Don haka, idan Tinubu ya ce zai yi tikitin Musulmi da Musulmi a kasa mai cike da rudani kamar tamu, idan 'yan Najeriya suka amince da shi kuma suka zabe shi, duk abin da ya faru, 'yan Najeriya za su fuskanci sakamakon aikinsu.
“Idan kuna da gwamnatin da fasto ne mataimakin shugaban kasa kuma ake kashe fastoci da masu ibada ku iya tunanin abin da zai faru idan muka samu tikitin Musulmi da Musulmi.
“Ya ragewa ’yan Najeriya su yi zabi, su zabe su, dukkanmu za mu fuskanci sakamakon tare."

Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

A tun farko, rahotanni da ke zuwa mana a yanzu sun nuna cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC) a zaben 2023, Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaben mai zuwa.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tinubu ya sake samun gagarumin goyon baya daga tsohon gwamna

Tinubu ya sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli, a garin Daura, jihar Katsina, yayin da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gaisuwar ban girma na babban Sallah, Channels Tv ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel