APC Ta Samu Ragin Mambobi, Shugabannin Gunduma a Sokoto Sun Koma PDP

APC Ta Samu Ragin Mambobi, Shugabannin Gunduma a Sokoto Sun Koma PDP

  • Sansanin PDP a jihar Sokoto ya samu karuwa yayin da wasu sabbin mambobi suka shigo cikinta daga jam'iyyar APC
  • Sabbin mambobin shugabanni ne na unguwar Dingyadi-Badawa a karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto
  • Daya daga cikinsu shine sakataren gundumar, Ummarun Hassan da mataimakin ma’ajin APC na gundumar Manu Abubakar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Bodinga, jihar Sokoto - Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a gundumar Dingyadi-Badawa a karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto sun sau ladansu, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP daga ta APC.

Kakakin jam'iyyar PDP na jihar, Hassan Sanyinnawal ne ya bayyana shigowarsu PDP a ranar Juma'a, 2 ga watan Satumba, Vanguard ta ruwaito.

Tarin mambobin APC sun sauya sheka zuwa PDP
APC Ta Samu Ragin Mambobi, Shugabannin Gunduma a Sokoto Sun Koma PDP | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

A wata sanarwar da ya fitar, Sanyinnawal ya ce daga cikin wadannan jiga-jigai akwai sakataren gundumar ta Dingyadi-Badawa, Ummarun Hassan da mataimakin ma'ajin APC na yankin, Manu Abubakar.

Kara karanta wannan

Da Dumi: Jami'ar IBB Dake Lapai Jihar Neja Ta Janye Daga Yajin Aikin ASUU, Tace Dalibai Su Koma Aji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran jiga-jigan na jam’iyyar APC a Sokoto da suka barranta da jam'iyyar sun hada da Barno Akamawa, jami’in hulda da jama’a na APC da wasu deliget hudu.

Deliget-deliget din dai su ne Shehu Abubakar, Sani Modi, Sunusi Imam, da Bello Alhaji, rahoton Daily Sun.

Haka kuma, daruruwan mambobi da magoya bayan jiga-jigan na siyasa sun furta kalmar shiga PDP tare da kwanayensu.

Alhaji Bello Goronyo, shugaban jam’iyyar na Sokoto ne ya karbi wadannan sabbin mambobi zuwa karkashin inuwar lemar PDP

Yace:

“Yanzu dukkanku ciakkun mambobi ne na jam’iyyar PDP, kuma ina mai tabbatar muku da cewa za a mutunta ku kamar yadda ake mutunta sauran mambobinmu a jihar."

Gabanin zaben 2023, ana yawan yawaitar sauya sheka daga jam'iyyu mabambanta domin cimma wata manufa ta siyasa ko samun daidaito.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a Osun Ya Sau Ladansa, Ya Yi Murabus

Kara karanta wannan

Tinubu ne ‘Dan takara Mafi Cancanta, Amma Akwai Abin da Nake Tsoro - Shugaban APC

A wani labarin, yanzu muke samun labarin cewa, tsohon dan majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Leye Odunjo, ya aje mukaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a jihar.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, a ranar Alhamis 1 ga watan Satumba, The Nation ta ruwaito.

Ya tura wasikar ne ta hannun shugaban jam’iyyar na jiha, Hon. Sikirulai Ogundele, inda ya bayyana dalilin aje mukamin da shawarin karan kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel