Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a Osun Ya Sau Ladansa, Ya Yi Murabus

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP a Osun Ya Sau Ladansa, Ya Yi Murabus

  • Jigon siyasa a jihar Ogun, kuma tsohon dan majalisar dokokin jihar ya bayyana ajiye aikinsa na mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a jihar
  • A rubuta wata wasika da ke bayyana manufarsa ta barin aiki, kana da irin kokari da bautawa jam'iyyar ta PDP a tsawon shekaru
  • Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida tun bayan kammala zaben fidda gwanin shugaban kasa, lamarin dake kara ruruwa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ogun - Yanzu muke samun labarin cewa, tsohon dan majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Leye Odunjo, ya aje mukaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a jihar.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, a ranar Alhamis 1 ga watan Satumba, The Nation ta ruwaito.

Jigon jam'iyyar PDP ya ajiye aiki saboda wasu dalilai
Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP a Osun ya sau ladansa, ya yi murabus | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya tura wasikar ne ta hannun shugaban jam’iyyar na jiha, Hon. Sikirulai Ogundele, inda ya bayyana dalilin aje mukamin da shawarin karan kansa.

Kara karanta wannan

Mu Kake Kira Yara, Zamu Koya Maka Hankali: Wike Ya Yiwa Ayu Raddi

A bangare guda na wasikar, ya yabawa Ogundele da sauran mambobin PDP na jihar bisa kaunarsa da ba shi goyon baya, inda ya ce zai yi kewar aiki dasu duka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A bangare guda, ya bayyana cewa, ya bautawa jam'iyyar PDP tun farkon kafa ta a 1998, kuma har yanzu shi dan a mutun ta ne, rahoton Punch.

Leye Odunjo ya kasance dan majalisar dokokin jihar Ogun na tsawon shekaru takwas, kuma ya taba tsaya takarar gwamna duk dai a jam'iyyar ta PDP.

Hakazalika, ya yi takarar majalisar wakilai ta kasa, ya kuma nemi kujerar sanata a zaben 2019 da ya gabata.

Kotun Daukaka Kara Ta Soke Batun Kwace Tikitin Oborevwori a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Delta Na PDP

A wani labarin na daban kuma, kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin da babbar kotun tarayya na ranar 7 ga watan Yuli, 2022 da ya kori kakakin majalisar Delta Sheriff Oborevwori a matsayin dan takarar gwamna a PDP a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

An Fara Sauraron Karar da Aka Kai Domin Karbe Takaran PDP Daga Hannun Atiku

Rahoton jaridar The Nation ya ce an aiwatar soke wannan hukunci na babbar kotu ne a yau Litinin 29 ga watan Agusta, 2022.

Wani kwamitin kotu karkashin jagorancin mai shari’a Peter Ige, ya bayyana cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraran karar da David Edevbie ya shiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel