‘Dan gwagwarmaya Ya Fadawa Atiku, Obi da Kwankwaso Hanyar Doke Tinubu a Saukake

‘Dan gwagwarmaya Ya Fadawa Atiku, Obi da Kwankwaso Hanyar Doke Tinubu a Saukake

  • Deji Adeyanju yana ganin babu yadda za ayi jam’iyyar hamayya ta karbe mulki daga hannun APC a zaben shugaban kasa
  • Shugaban na kungiyar Concerned Nigerians group ya ba ‘yan takaran adawa su hada-kai domin su iya dole Bola Tinubu
  • Adeyanju yana ganin abin da ya fi dacewa shi ne duk sauran ‘yan takaran 2023 su bi bayan mutum daya a zabe mai zuwa

Abuja - Shugaban kungiyar Concerned Nigerians group, Deji Adeyanju yace akwai bukatar jam’iyyun adawa su dunkule kafin a kifar da gwamnatin APC.

Leadership ta rahoto Kwamred Deji Adeyanju yana cewa taron dangin Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwanso ne kawai zai doke Bola Tinubu.

Adeyanju ya tunawa ‘yan siyasar da ke neman takara cewa ba a karbar mulki a Afrika da zakin baki, yace abin da mutane ke bukata shi ne a cika tumbinsu.

Jaridar ta shirya wani taro a shafinta na @LeadershipNGA a Twitter, aka gayyaci Adeyanju domin suyi bayani a game da sha’anin zaben 2023 da shugabanci.

A cewar Adeyanju, ya sa ido wajen zabuka kalla 39 da aka shirya a Najeriya da wajen kasar, kuma ya fahimci dole PDP, LP da NNPP duk su tunkari APC gaba daya.

‘Dan gwagwarmayar yana ganin ‘yan takaran na 2023 ba su shirya kabar mulkin Najeriya ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku
Atiku Abubakar mai takara a PDP Hoto: @Atiku
Asali: Facebook

Yadda aka cin zabe a Afrika

“Ba a cin zabe da kwakwalwa a Afrika. Abin da ke sa a ci zabe a wannan yankin na Duniya shi ne kabila, addini, murdiya, saida kuri’a da raba kudi da abinci.”
“Abin da jam’iyyun hamayya suke yi ba zai taimaka masu ba. Watakila Gwamna Wike ba zai taimakawa Atiku ba, idan bai tabbata cewa zai lashe zabe ba.”

“Babu wani wanda zai so a ce bai yi nasara ba. Peter Obi ya cancanta, amma ba zai yiwu Atiku ya janye masa takara ba. Dole ne su hada-kai. Haka abin yake.”

Kwankwaso yana tare da APC?

An rahoto ‘dan gwagwarmayar yana zargin Rabiu Kwankwanso da yi wa Tinubu aiki a kaikaice domin ‘dan takaran na NNPP bai son Atiku ya yi nasara a 2023.

A cewarsa, wanda zai ci zabe shi ne wanda ya samu gagarumar nasara a Kano, Kaduna da Katsina. Duka wadannan jihohin dai suna yankin Arewa ne.

Menene silar arzikin Tinubu?

Kwanaki mun kawo rahoto inda aka ji Deji Adeyanju yace dole ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya fadawa ‘yan Najeriya inda ya samo dukiyarsa.

Tun bayan zaman Bola Tinubu ɗan takarar APC na 2023, masu sharhin siyasa suke ta saka alamar tambaya kan dukiyarsa, lafiyarsa da kuma inda ya yi karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel