Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas

  • Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kame wani matashi da ke ikrarin cewa shi jami'an sojan Najeriya ne
  • An kama shi dauke kayayyaki daban-daban na sata, yanzu haka za a gurfanar dashi a gaban kotu
  • Ana yawan samun 'yan Najeriya da ke amfani da kakin soja wajen damfarar jama'a, musamman a kudu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Wani mutum dan shekaru 39 mai suna Andy Edwards ya shiga hannun jami'an 'yan sanda bisa zargin ikrarin shi kyaftin din soja ne a Legas, inda ya iakata fashi da makami.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kama matashin a ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar, Daily Nigerian ta ruwaito.

An kama wani sojan bogi a jihar Legas
Yadda Aka Kame Wani Matashi da Ke Ikrarin Shi Soja Ne, Ya Tafka Sata a Jihar Legas | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Hundeyin, ya shaida cewa, wanda aka kamen soja ne bogi, wanda ke fitowa a matsayin mai mai sana'ar talla. Kana yana gayyato 'yan mata da sunan zai dauke su aiki kafin daga bisani ya sace motocinsu ko dan abinda suka zo dashi

Kara karanta wannan

Hankali ya tashi yayin da 'yan bindiga suka sace wani dan kasar waje, suka kashe soja a Kaduna

Ya ce an kwamushe Andy ne biyo bayan dogon bincike da jami'ai suka yi bayan da aka shigar da karar ya sace motar wata mata kirar Lexus RX330 SUV, rahoton Daily Sun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Hundeyin:

“Bincike ya kai ga bankado wata mota kirar Ford Edge SUV mai lamba KRD 276 EG, keken dinke daya da na’urar POS daya mai dauke katunan SIM guda shida a gidan wanda ake zargin.
“Haka nan kuma an kwace kakin kakin soja guda biyu da lambar mota guda - AFL 469 GD.
“Yayin da ake ci gaba da bincike, ana kira ga mai mota kirar Ford SUV din da zo ya ba da bayani ya amshi kayarsa. Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya bayan kammala cikakken bincike.”

Hundeyin ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar Legas ci gaba da jajircewar jami’an 'yan sanda wajen wanzar da zaman lafiya da kare rayukan al'umma.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotunan Daurin Auren Wasu Yan Najeriya A Dubai Ya Yadu, Sun Yi Shaglin Bikinsu A Saukake

Duk da kokarin Hisbah na hana shan barasa, 'yan Najeriya sun kwankwadi ta N600bn a wata shida

A wani labarin, wani rahoton da kafar yada labarai ta BBC ta fitar ya ce, akalla barasar N599.11 ne 'yan Najeriya suka kwankwada a cikin watanni shida kacal na farkon 2022.

Rahoton ya fito ne daga kamfanonin barasa hudu na Najeriya, kuma ya mai da hankali ne daga watan Janairun bana zuwa watan Yunin da ta gabata.

Guinness da Champion na daga cikin kamfanonin hudu, kuma sun ce kwalliya ta biya kudin sabulu, domin kuwa kamfanonin barasa a Najeriya sun samu riba mai tsoka a wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel