2023: Shin Da Gaske Ne Likitan Tinubu Ya Bashi Shawara Ya Ajiye Takara? Na Hannun Daman Jagaban Ya Magantu

2023: Shin Da Gaske Ne Likitan Tinubu Ya Bashi Shawara Ya Ajiye Takara? Na Hannun Daman Jagaban Ya Magantu

  • Wani dan kudu, Maxwell Nwadike, ya yi ikirarin cewa ana yi wa Bola Tinubu matsin lamba ya ajiye takarar shugaban kasarsa
  • Nwadike cikin wani rubutu da ya yi a Twitter, ranar 25 ga watan Agusta, ya yi ikirarin cewa matsin lamban na zuwa ne daga likitan Tinubu a kasar Faransa
  • Amma, Joe Igbokwe, na hannun daman tsohon gwamnan na Legas ya karyata ikirarin Nwadike kuma aka ce labarin kanzon kurege ne

Joe Igbokwe, daya cikin na hannun daman Asiwaju Bola Tinubu, ya yi martani kan ikirarin da wani Maxwell Nwadike ya yi na cewe likitan dan takarar shugaban kasa na APC ya shawarce shi ya ajiye takararsa na 2023.

Bola Tinubu
2023: Da Gaske Ne Likitan Tinubu Ya Bashi Shawara Ya Ajiye Takara? Na Hannun Daman Jagaban Ya Magantu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

A cewar Nwadike a wani rubutun da ya yi a Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, ya yi ikirarin cewa yanayin lafiyar Tinubu a halin yanzu ne yasa likitansa ya bashi wannan shawarar.

Kara karanta wannan

Ni ba barawo bane: Tinubu ya fadi sana'ar da yake ya tara makudan biliyoyi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana kan ikirarin, Igbokwe a wani rubutu da ya yi a Facebook a ranar Juma'a, 26 ga watan Agusta, ya bayyana batun a matsayin tsantsagwaran karya.

Igbokwe ya fayyace cewa "kareraki, labaran bogi, farfaganda, zagi, bita da kulli da sauransu ba za su taimakawa kowa cin zaben shugaban kasa na 2023 ba."

Ya ce abin da kawai zai iya taimakawa mutum cin zabe sune 'ayyukan kirki da mutum ya yi a baya, kwarewa, ilimi, zumunci, kusantar talakawa, sanin mutane a kasa da kasashen waje, magoya baya da abota da aka gina na tsawon shekaru'.

Igbokwe ya kammala rubutunsa na Facebook da cewa:

"Asiwaju ya dade yana aiki kuma yana shirin darewa kujerar shugaban kasa tun kafin shekarar 1993 ...".

Olusegun Obasanjo Ya Ce Bangaren Tinubu Sun Masa 'Sharri'

A wani rahoton, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gargadi wasu magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rudani: Malamin addini ya hango matsala, ya ce sojojin Najeriya za su shiga yajin aiki

Tinubu da wasu jiga-jigan APC sun ziyarci Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban binrin Jihar Ogun, a ranar Laraba.

Cikin wadanda suka yi wa Tinubu rakiya akwai tsaffin gwamnonin jihar Ogun, Olusegun Osoba da Otunba Gbenga Daniel, dan kasuwa kuma tsohon shugaban riko na APC, Cif Bisi Akande da Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel