Daga Karshe Dai Dan Takarar APC Tinubu Ya Bayyana Inda Yake Samo Kudi

Daga Karshe Dai Dan Takarar APC Tinubu Ya Bayyana Inda Yake Samo Kudi

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana hanyar da ya bi ya samo makudan kudaden da yake kashewa a yanzu
  • Ya kuma nemi duk wani biloniya a Najeriya da ya fito ya fadi hanyar da ya bi ya samo kudaden da yake fankama dasu
  • 'Yan Najeriya na mamakin yadda wasu 'yan siyasar Najeriya kan ina suke samo kudaden da suke kashewa

Dan takarar shugaban kasa ajam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana gaskiyar sana'ar da yake yi kuma har ya tara dukiya mai yawa.

Tinubu ya yi nuni da cewa, duk wani wayayyen dan Najeriyan da kwashi kudinsa N1.8m kacal ya zuwa hannun jari a kamfanin Apple a 1980 to ya zuwa yanzu ya mallaki sama da Naira Tiriliyan 10.

A wani rubutu ta Facebook da Joe Igbokwe ya yada, Tinubu ya bayyana cewa ya mallaki miloniyoyin daloli akalla shekaru 10 kafin ya zama gwamnan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Idan Na Sauka Daga Kan Karagar Mulki, Zan Koma Mawaki Ne inji Gwamnan APC

Tinubu ya bayyana silar samo arzikinsa
Daga karshe dai dan takarar APC Tinubu ya bayyana inda yake samo kudi | Hoto: Joe Igbokwe
Asali: Facebook

Shugaban na jam’iyyar APC na kasa ya bayyana cewa, shi mai arziki ne tun lokacin da yake rike da mukamin shugaban NADECO.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Don Allah ku fada ma matasa gaskiya.Ni Asiwaju Tinubu na mallaki miliyoyin daloli tun ina shugaban NADECO akalla shekaru 10 kafin na zama gwamnan jihar Legas. Ya kamata wasu ma su fito su bayyana silar mallakar biliyoyinsu."

Ya kuma bayyana cewa, shi ba barawo bane, domin a can baya da mutane ke sayen manyan motoci na miliyoyi suna hawa, shi ya yi dabarar zuwa hannun jarinsa a kamfanin da zai samar masa da kudi a gaba.

A cewar Tinubu, ire-irensa da suka jari a kamfanonin na'ura, a kowace rana suna iya samun dala 1000 ko fi daga hannun jarin.

Bola Tinubu Shugaban Kasan Najeriya Na Gaba, Inji Gwamnan Su Buhari, Masari

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

A wani labarin, Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya bayyana kwarin giwarsa kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Masari ya bayyana karara cewa, Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa a 2023 “Insha Allahu.”

Gwamnan ya yi wannan magana ne yayin hira da gidan talabijin na TVC, a jiya Laraba 24 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.