Olusegun Obasanjo Ya Ce Bangaren Tinubu Sun Masa 'Sharri'

Olusegun Obasanjo Ya Ce Bangaren Tinubu Sun Masa 'Sharri'

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ragargaji wasu magoya bayan dan takarar APC, Bola Tinubu saboda yi wa mutane karya
  • Tinubu ya gana da Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta a ranar Laraba 17 ga watan Agusta inda mutanen biyu suka tattauna
  • Amma wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyar APC da suka yi ikirarin sun hallarci taron sun ce tsohon shugaban kasar ya goyi bayan takarar Tinubu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya gargadi wasu magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Daily Trust ta rahoto.

Tinubu da wasu jiga-jigan APC sun ziyarci Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, babban binrin Jihar Ogun, a ranar Laraba.

Tinubu da Obasanjo.
Olusegun Obasanjo Ya Ce Bangaren Tinubu Sun Masa 'Sharri'. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

'Suna Shirin Kashe Ni' Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Ya Aike da Sako Ga IGP, Ya Fallasa Sunaye

Cikin wadanda suka yi wa Tinubu rakiya akwai tsaffin gwamnonin jihar Ogun, Olusegun Osoba da Otunba Gbenga Daniel, dan kasuwa kuma tsohon shugaban riko na APC, Cif Bisi Akande da Kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila.

Obasanjo da Tinubu dukkansu ba su yi magana da manema labarai ba bayan taron.

Amma, kwana guda bayan taron, Gbajabiamila ya yi magana kan abinda ya faru wurin taron tsakanin Obasanjo da Tinubu.

Ya ce Obasanjo ya ce furta kalamai na karfafa gwiwa game da takarar Tinubu har ma ya yi wa dan takarar shugaban na APC addu'a.

Abinda wasu da ke ikirarin goyon bayan Tinubu ke fada ba 'alheri' bane - Obasanjo

Amma, cikin wata sanarwa ta hannun mataimakinsa na musamman a bangaren watsa labarai, Kehinde Akinyemi, a ranar Asabar, Obasano ya ce kalaman da ke fitowa daga bakin wasu da ke ikirarin goyon bayan Tinubu ba "alheri" bane.

Kara karanta wannan

2023: Fani-Kayode Ya Gana Da Tinubu A Abuja, Ya Aika Wa PDP Sako Mai Karfi

Tsohon shugaban kasar ya ce abubuwan da suka tattauna yayin ziyarar "sun fi alaka yan uwantaka maimakon siyasa" kuma Bola Tinubu ya bukaci kada su yi magana da yan jarida, shima Cif Obasanjo ya yarda ba zai ce komai ba.

Obasanjo ya ce:

"Wadanda suke ikirarin cewa sun hallarci taron kuma suke fitar da sanarwa kan tattaunawar da aka yi suke danganta abin da ban fada ba da ni makiyan bakon nawa ne kuma hakan ba alheri bane ga ziyarar."

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Ya Koka Kan Tsadar Rayuwa, A Yayin Da Farashin Kaya Ke Cigaba da Tashi A Kasar

A wani rahoton, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Olusegun Obasanjo a ranar Talata 2 ga watan Agusta ya shiga jerin miliyoyin yan Najariya da ke kokawa kan tsadar rayuwa da wasu abubuwan.

Obasanjo ya bayyana cewa yana keta gumi sosai saboda tsadar dizal wanda ke shafar kasuwancinsa da wasu kasuwancin a sassan kasar.

Kara karanta wannan

2023: Ka Maye Gurbin Shettima Da Kirista, Matasan APC Suka Fada Wa Tinubu

Daily Trust ta rahoto cewa tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a wurin taron masu kiwon kifi na kudu maso yamma da aka yi a dakin karatu na Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (OOPL) a Abeokuta, Jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel