2023: Wike Zai Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zabe Cikin Sauki, Masari

2023: Wike Zai Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zabe Cikin Sauki, Masari

  • Na hannun daman Bola Tinubu, wanda suke tare yanzu haka a Landan ya bayyana sakamakon taron Wike da Tinubu
  • Ibrahim Masari ya ce suna da kwarin guiwar gwamna Wike na Ribas zai taimaka wajen cicciɓa Tinubu ya shige fadar shugaban kasa a 2023
  • Jigon APC, wanda ya tabbatar da ganawar jiga-jigan siyasan biyu, ya ce da ikon Allah tun Asuba Tinubu zai lashe zaɓe

Abuja - Alhaji Ibrahim Masari, na hannun daman ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana fatan da suke bayan ganawa da gwamnan Ribas Nyesom Wike a birnin Landan.

Vangaurd ta rahoto cewa Masari ya ce suna da kwarin guiwa bayan zaman Landan, gwamna Wike zai yi aiki tuƙuru domin nasarar Tinubu a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Mu ba butulu bane: Tinubu ne zan gaji Buhari a 2023, Insha Allahu, Masari ya bayyana dalilai

Gwamna Wike da Bola Tinubu.
2023: Wike Zai Taimaka Wa Tinubu Ya Lashe Zabe Cikin Sauki, Masari Hoto: Bola Tinubu/facebook
Asali: Twitter

Alhaji Masari, wanda ya yi jawabi daga Landan, ya shaida wa BBC Hausa a ranar Laraba cewa dagaske ne Bola Tinubu ya gana da Wike kuma zasu cigaba da tattauna wa lokaci bayan lokaci.

A cewar Masari, "Taron ya maida hankali ne kan zaɓen shugaban ƙasan 2023 kuma da izinin Allah zamu yi aiki tare da mai girma gwamna Nyesom Wike, zai taimaka kuma zamu lashe zaɓe cikin ruwan sanyi Insha Allahu."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin gwamna Wike zai koma APC ne?

Yayin da aka tambaye shi ko Wike na da nufin sauya sheka zuwa APC domin sararawa wajen taimaka wa Tinubu, Masari ya ce ba zai ce komai kan ko gwamnan zai koma APC ba.

Sai dai ya ƙara da cewa gwamna Wike ba ya bukatar ya fice daga PDP kafin ya taimaka wa wanda ya yi niyya a zuciyarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

Daily Trust ta ruwaito Masari ya cigaba da cewa:

"Saboda Wike ba karamin ɗan siyasa bane, gwamna ne sukutum kuma yana juya wasu jihohin ban da jiharsa. Mutumin kirki ne ga mutanen sa kuma ya kulla alaƙa mai kyau da makusantansa, da ikon Allah zai taimaka mana."

Shin wannan ƙawancen zai yi ƙarko?

Haka nan, da aka tambaye shi ko yana ganin wannan kawancen zai yi ƙarko duba da Atiku Abubakar, na cigaba da faɗi tashin lalubo hanyar sasantawa da Wike, Masari ya ce:

"Allah ƙaɗai ya san abin zai faru nan gaba, amma abinda muke gani a zahirance zamu haɗa karfi da Wike kuma zai mana amfani matuka. Idan baku manta ba APC ce da jawa kanta rashin nasara a Bauchi."
"Haka ta faru a Adamawa saboda haka abinda nake so ku gane shi ne, mutum zai iya taimaka maka ko da bai shigo jam'iyyar da kake ciki ba."

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

"Bugu da kari, duba da yadda ƴan Najeriya suka rungumi Bola Tinubu, zan iya tabbatar muku da cewa shi zai lashe zaɓe ko babu wanda ya taimake shi. Sai dai wata karin magana tace, ko kana da kyau ka ƙara da wanka."

A wani labarin kuma Yan Daban PDP Sun Kai Farmaki Wurin Taron Da Aka Shirya Domin Atiku Abubakar

Wasu yan daba sun tarwatsa ɗakin taron da aka shirya domin tabbatar da goyon bayan Atiku Abubakar a jihar Ribas.

Wata ƙungiya ta shirya taro a garin Bori, ƙaramar hukumar Khana da Ribas da nufin bayyana wa duniya mubaya'arta ga Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel