A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Sule Lamido

A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Sule Lamido

  • Rikicin da ya kunno kai tsakanin yan bangaren Atiku Abubakar da Nyesom Wike ya ki ci, ya ki cinyewa
  • Gwamna Sule Lamido ya jaddada cewa a rabu da Wike yayi abinda ya ga dama, babu laifin da akayi masa
  • Gwamna Wike ya shiga adawa da Atiku ne bisa rashin zabensa matsayin dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na PDP

Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce babu wani laifi da aka yiwa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kuma a rabu da shi yayi abinda ya ga dama.

Lamido ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar Channels TV

Yace jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP na da kundin tsarin mulki da dokoki kuma zabe akeyi don zaben duk wani dan takara.

Kara karanta wannan

Hantar Atiku da PDP Ta Kada Bayan Samun Bayanin Zaman Tinubu da Wike a Landan

A cewarsa:

"Mutane na takarar Kansila; wasu su yi nasara, wasu su fadi. Hakazalika na shugaban karamar hukuma da Gwamna. Saboda haka menene matsalar Wike? A ra'ayina wa yayi wa Wike laifi?"
"An yi zaben fidda gwani kuma shi Wike da kansa yace zaben na gaskiya ne babu magudi. Saboda haka menene matsalar"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sule Lanido
A Rabu Da Wike, Yayi Duk Abinda Ya Ga Dama: Sule Lamido Hoto: ChannelsTV

Lamido yace Wike ya daina tunanin yafi kowa karfi a siyasar jihar Rivers don shine Gwamna.

Yace:

"Wike mutum daya ne fa. Ban tunanin don kawai gwamna ne yana da ikon komai a Rivers. Mutan Rivers da PDP na da hakkinsu."
"A rabu da Wike. Yana da daman yin abinda yake so. Shi ke da komai a Rivers."

Wike Da Wasu Gwamnonin PDP Sun Tafi Turai Ganawa da Tinubu Ranar Litinin, Majiya

Labarai sun bayyana cewa Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya tafi nahiyar Turai ganawa da dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Masoyin Inyamurai ne: Jigon NNPP ya fadi abin da Kwankwaso ya shirya yiwa Inyamurai

TheCable ta ruwaito cewa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom; gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde; gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu da wasu manyan jigogin PDP na hallare a zaman.

Wike da tawagarsa sun tafi Turai ne da safiyar Litinin, 22 ga Agusta, 2022.

A riwayar Vanguard, ana hasashen wannan ganawa bai rasa alaka da goyon bayan Tinubu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel