An Gano Wanda ya yi Karambani, Ya kai Atiku da Tambuwal Kotu da Sunan Wike

An Gano Wanda ya yi Karambani, Ya kai Atiku da Tambuwal Kotu da Sunan Wike

  • Cosmos Ndukwe yace shi ne ya shigar da kara a kotu, saboda a hana Atiku Abubakar takara
  • ‘Dan siyasar ya shaida cewa ya je kotu ne a dalilin sabawa dokar PDP da aka yi a shirin zaben 2023
  • Ndukwe ya rike Kwamishina, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da kujerar Majalisa a Abia

Abuja - Ba kowa bane ya shigar da kara saboda a hana Atiku Abubakar yin takara a karkashin jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa illa Dr. Cosmos Ndukwe.

Vanguard ta kawo rahoto cewa Dr. Cosmos Ndukwe shi ne ainihin wanda ya dumfari kotu, yana karar Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal, INEC da PDP.

Ndukwe ya shaidawa Duniya cewa shi ne wanda ya shigar da wannan kara ba Nyesom Wike ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban PDP ya Nunawa Atiku Abin da Zai Hana Sa Kai Labari a 2023

‘Dan siyasar ya yi wannan karin bayani ne bayan an ji Gwamnan Ribas ya fito yana cewa babu ruwan shi da karar da aka shigar a kotun tarayya a Abuja.

Wike wanda ya gaza samun tutan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya nesanta kansa da karar, ya zargi mutanen Atiku Abubakar da wannan aikin.

Abin da kotu ta sani shi ne Newgent Ekamon da Nyesom Wike ne suka shigar da karar. Alal hakika, Honarabul Ndukwe ne ya yi hakan a bayan fage.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tambuwal da Wike
Aminu Tambuwal da Nyesom Wike Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Ni ne nan ba kowa ba - Ndukwe

Da aka yi hira da shi a Vanguard, tsohon mataimakin shugaban majalisar dokoki na jihar Abia yace shi ne ya yi karar Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal

A cewar ‘dan siyasar, ya kai kara zuwa kotu ne saboda jam’iyyarsu ta PDP ta sabawa dokarta da ta tsaida Atiku a matsayin ‘dan takaran shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

Dr. Ndukwe yake cewa PDP ta saba da tsarin kama-kama domin tabbatar da adalci a jam’iyya, amma aka yi watsi da wannan tsari a zabe mai zuwa na 2023.

Ba yau Ndukwe ya fara ba

Ndukwe wanda ya taba rike kujerar shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati yace kafin yanzu ya shigar da kara ganin PDP ta ki kai takara zuwa Kudu.

Da yake bayani, Ndukwe yace ya yi nasara a babban kotun tarayya, amma daga baya kotun daukaka kara ta ba jam'iyyarsa gaskiya, don haka ya tafi kotun koli.

Ana sa ran nan da kwanaki 45 za a saurari wannan karar a kotun Allah ya isa domin raba gardama. Ndukwe yana sa ran za a hana PDP ta ba 'Dan Arewa tutarta.

Za ayi sulhu kafin zabe

Kun samu labari Gwamnoni sun sa baki a matsala, su na neman sasanta Atiku Abubakar da Nyesom Wike, kowane ya kawo wadanda za su shiga kwamitin.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP A Kano Na Kara Dagulewa, Mohammed Abacha Ya Maka Jam'iyya Da INEC A Kotu Kan Tikitin Takarar Gwamna

Ana zargin akwai wani tsohon Gwamna da wani tsohon soja da suke kawo matsala a yunkurin da ake yi na ganin an yi sulhu tsakanin jiga-jigan kafin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel