An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

  • Jagororin PDP sun kafa kwamiti na mutane 14 da za su sasanta rigimar da ta addabi Jam’iyyar
  • An samu sabani tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike kan takarar shugaban kasa
  • Ana sa ran wannan kwamiti zai duba silar rikicin, ya kuma ba Atiku shawarar hanyar da za a bi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kwamitin mutum 14 da Atiku Abubakar da Nyesom Wike suka kafa domin kokarin dinke barakar jam’iyyar PDP zai fara aiki a cikin makon nan.

Rahoton Premium Times yace wannan kwamiti zai soma aiki ne a ranar Litinin, 15 ga watan Agusta 2022 a Abuja domin ya magance rikicin cikin gidan.

‘Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar da Gwamnan Ribas sun yarda a kafa kwamitin sulhu da suka yi wani zama.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike ya Kai Atiku da Tambuwal Kotu, yace Shi ne Asalin ‘Dan takaran PDP

A karshen taron da aka yi a gidan Farfesa Jerry Gana, shugabannin na PDP sun amince da yadda za ayi kokarin magance sabanin da aka samu a jam’iyya.

Kwamitin zai duba koke-koken Gwamna Wike da sauran jagororin PDP da ke tare da shi, sannan za su ba su Atiku shawarwarin yadda za a bullowa lamarin.

Su wanene aka sa a kwamitin?

Daga bangaren Wike, ya bada sunayen tsofaffin gwamnoni Segun Mimiko, Donald Duke, da Ibrahim Dankwambo a matsayin wadanda za su wakilce shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku
Atiku Abubakar a Jigawa Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Haka zalika akwai tsohon Ministan shari’a, Mohammed Bello Adoke da kuma Hon. Nnena Ukeje.

Shi kuwa Atiku Abubakar ya bada sunayen tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da gwamnan Adamawa, Umaru Fintiri a matsayin mutanensa.

Jaridar ta rahoto cewa sauran wadanda ‘dan takaran ya bada a kwamitin sun kunshi Liyel Imoke, Eyitayo Jegede da tsohon abokin takararsa, Sanata Ben Obi.

Kara karanta wannan

Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

Akwai sauran mutane biyu daga kowane bangare da za su yi aikin sasanta rigimar cikin gidan. Gwamna Umaru Fintiri zai jagoranci aikin kwamitin sulhun.

Vanguard ta rahoto cewa akwai wani tsohon Gwamna da wani tsohon soja da suke kawo matsala a yunkurin da ake yi na ganin an yi sulhu kafin zaben 2023.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamnoni sun sa baki a matsala, su na neman kawo gyara.

Ana kokarin kawo maslaha

A baya an ji cewa wadanda ke tare da Wike suna so a tunbuke Iyorchia Ayu daga kujerar shugaban PDP. Kwamitin duk zai duba wadannan bukatu da wasunsa.

A yammacin Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022 ne aka soma yin zama domin ayi sulhu tsakanin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike gabanin shiga kamfe.

Haduwar ‘dan takaran shugaban kasar da gwamnan na Ribas na zuwa ne jim kadan bayan ‘yan majalisar amintattu na BoT sun yi zaman dinke baraka a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Biki Bidiri: Hotuna Da Bidiyon liyafar Sa Lalle Na Surayya Sule Lamido, An Sha Rawa An Girgije

Asali: Legit.ng

Online view pixel