An Sake Samun Lauyan da Ya Kai INEC Kara a Kotu Saboda Takarar Bola Tinubu

An Sake Samun Lauyan da Ya Kai INEC Kara a Kotu Saboda Takarar Bola Tinubu

  • Barista Mike Enahoro-Ebah zai yi shari’a da hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC
  • Lauyan ya yi amfani da FOI, ya nemi INEC ta damka masu duk wasu takardun takarar Bola Tinubu
  • Ganin har yanzu bai samu biyan bukata ba, Mike Enahoro-Ebah ya nemi kotu ta tursasa INEC

Abuja - Mike Enahoro-Ebah, wanda kwararren Lauya ne a Abuja ya shigar da karar hukumar INEC a kotu a game da takardun takarar Asiwaju Bola Tinubu.

Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta 2022 cewa Lauyan ya kai karar ne domin INEC ta fitar da takardun CTC na ‘dan takaran na APC.

Mike Enahoro-Ebah ya kuma nemi kotu ta umarci hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar da takardun shiga takara a 1999 da 2003 da Tinubu ya gabatar.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

‘Dan siyasan ya yi takarar kujerar gwamna a zaben 1999 da na 2003, ya kuma yi nasarar zarcewa a kan kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar AD.

A halin yanzu Bola Tinubu yana neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.

Lauyan ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1337/2022 a babban kotun tarayya, yana so INEC ta mallaka masa takardun EC 13A da EC 9 na Bola Tinubu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Masallaci Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Haka zalika Mike Enahoro-Ebah ya bukaci Alkali ya ba shi damar ganin takardun da Bola Tinubu ya mikawa INEC kafin ya shiga takarar gwamna a jihar Legas.

Lauya ya yi amfani da FoI

A cewar Lauyan, ya bukaci INEC da wannan bukata a watan Yuli, yana mai dogara da dokar FOI ta 2011. FOI ta ba ‘dan kasa samun duk bayanan da yake nema.

Kara karanta wannan

Wike Ya Gayyaci Jigon APC, Wamakko, Ya Kaddamar Da Ayyuka A Rivers

Abin da dokar tace shi ne idan mutum ya nemi samun bayanai, zai jira na tsawon makonni biyu, bayan nan zai iya neman kotu ta sa baki idan har ya ji shiru.

Idan aka yi la’akari da sashe 29(4) na dokar zabe da dokar FOI ta kasa, Enahoro-Ebah yace an aikata laifi idan aka boyewa Duniya takardun 'dan takaran na APC.

Ba mu da labari ko kotun da ke zama a Abuja ta sa ranar da za a fara sauraron wannan shari’a.

Shari'ar IGP da kungiya

Kwanakin baya an samu irin wannan labari, Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy, ta kai karar Sufetan ‘Yan Sanda a kotu.

Kungiyar ta na so tayi shari’a da shugaban ‘yan sandan ne saboda ya ki yin shari’a da Bola Ahmed Tinubu mai neman takara a APC, wanda ake zargi da laifi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel