Za a jikawa Jam’iyyar APC aiki, an maka IGP a kotu kan binciken Tinubu da aka yi a 1999

Za a jikawa Jam’iyyar APC aiki, an maka IGP a kotu kan binciken Tinubu da aka yi a 1999

  • An samu wata kungiya ta shigar da karar Sufetan ‘Yan Sanda a kotu saboda an ki binciken Bola Tinubu
  • Kungiyar ta ce ya kamata ‘Dan takaran APC watau Tinubu ya bayyana a kotu a kan batun takardunsa
  • Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy za tayi shari’a da IGP ne a garin Abuja

Abuja - Wata kungiya mai zaman kan ta mai suna Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy, ta kai karar Sufetan ‘Yan Sanda a kotu.

This Day ta ce wannan kungiyar ta na so tayi shari’a da shugaban ‘yan sandan ne saboda ya ki yin shari’a da Bola Ahmed Tinubu mai neman takara a APC.

Ana zargin Tinubu ya yi karya a game da takardunsa, don haka Incorporated Trustees of Center for Reform and Public Advocacy ta nemi a maka shi a kotu.

Kara karanta wannan

Mai dakina ta na ajiye Bible dinta a gefen Qur’ani na, kuma a kwana lafiya inji Tinubu

Mike Nwankwo shi ne Lauyan da ya tsayawa kungiyar a babban kotun tarayya mai zama a Abuja.

A madadin kungiyar, Lauyan ya ce sun kai Sufeta Janar kara ne saboda ya gagara daukar mataki a kan korafin da aka gabatar a game da takarar Bola Tinubu.

Binciken da aka yi a 1999

Kamar yadda Nwankwo ya fadawa kotu, majalisar dokokin Legas ta taba zargin ‘dan takaran shugaban kasar da laifi, a lokacin yana gwamna tun a 1999.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

IGP Alkali Baba
Shugaban 'Yan Sanda na kasa Hoto: alltimepost.com
Asali: UGC

Lauyan kungiyar ya kafa hujja da sass ana 214 da 215 na kundin tsarin mulki, da sashe na 4 na dokar ‘yan sand ana shekarar 2022 wajen shigar da wannan kara.

An ji Nwankwo yana mai cewa nauyin bincike da hana laifi da gurfanar da wadanda ake tuhuma ya rataya a kan rundunar ‘yan sandan kasa da IGP yake jagoranta.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso bai cire ran hada-kai da Peter Obi ba, duk da 'Yan hana ruwa gudu

The Cable ta ce a wannan shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1058/2022, kungiyar ta roki kotu ta tursasa wanda ake zargi da ya dauki mataki a kan ‘dan takaran.

Me dokar Najeriya ta ce?

Sashe na 31 da 32 na dokar aikin ‘yan sanda da wani sashe na 3 a dokar CJA na shekarar 2015 ya bada dama wannan kungiya ta tursasawa Sufeta Janar na Najeriya.

A doka, aikin ‘yan sanda ne a hukunta masu laifi ko wadanda akalla ake zargi. Bayan bincike, ‘yan sanda za su tuntubi AGF domin neman shawara a bisa doron doka.

Abokin takarar Tinubu

Ku na da labari cewa har yanzu ‘dan takaran shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai tsaida abokin tafiyarsa ba, alhali a watan nan wa'adin INEC zai cika.

Kungiyoyi su na ta fitowa su na bada shawarar wanda ya kamata Ahmed Tinubu ya dauka. An yarda cewa 'dan takaran zai dauko abokin tafiyarsa ne daga Arewa.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun dumfari kotu, su na so a hana Atiku, Tinubu da Obi tsayawa takara a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng