'Yan ci da addini: Kungiyar kiristoci ta fara ba da lambobin shaida ga sahihan malamanta

'Yan ci da addini: Kungiyar kiristoci ta fara ba da lambobin shaida ga sahihan malamanta

  • Wata kungiyar addini da aka fi sani da kungiyar limaman addinin Kirista a Najeriya (CACN) ta sanar da matakin bayar da katin shaida ga malamanta a Najeriya
  • Kungiyar ta bayyana cewa ta dauki matakin ne sakamakon martani daga abin kunyar da wasu bishop suka ja wa kiristoci a wajen kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC
  • CACN ta yi la'akari da cewa kwararrun kungiyoyi irinsu NBA da ma na likitocin kasar suna da katunan tantance mambobi don haka, babu abin da ya isa ya hana malamai yin haka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Onitsha, jihar Anambra - Kungiyar malaman addinin Kirista a Najeriya ta fara ba da katunan tantance ga daukacin malaman addinin Kirista a kasar.

Kungiyar ta ce bayyanar wasu mutane sanye da tufafin bishop yayin bikin kaddamar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, a Abuja kwanan nan ne ya jawo hakan.

Kara karanta wannan

Gwmnatin Tarayya Ta Saya Wa Jamhuriyyar Niger Motocin Naira Biliyan 1.4

Za a fara ba malaman kirista lambar shaida
'Yan ci da addini: Kungiyar kiristoci ta fara ba da lambobin shaida ga sahihan malamanta | Hoto: thenigerialawyer.com
Asali: UGC

Ta ce irin martanin da wannan lamarin ya haifar da kuma abin kunyar da ya haifar ga kungiyar Kiristoci ta Najeriya ya sa ya zama wajibi a fara bayar da katin ga dukkan limaman Kirista a Najeriya domin a samu sauki wurin tantance su.

Ko’odinetan CACN na kasa, Mai Shari’a Alpha Ikpeama, da Sakatarenta na kasa, Bishop Joseph Ajujungwa, ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka ba manema labarai a Onitsha ta jihar Anambra, ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun ce za a gudanar da atisayen ne tare da hadin gwiwar kafafen yada labarai na Bible Family Christian Media da aka fi sani da Bible Media, cibiyar bincike da yada labaran kiristoci ta duniya.

Kungiyar ta yi nuni da cewa, idan kwararrun kungiyoyi, kamar kungiyar lauyoyi ta Najeriya da kuma likitocin kasar suna da katunan tantance mambobi, babu abin da zai hana malamai yin hakan.

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

A baya, dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya mayar da martani ga masu suka, wadanda suka zargi tawagarsa da yin hayar masu yawo a titi da kuma shirya su a matsayin malaman Kirista a wajen gabatar da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima a Abuja.

A cikin wata sanarwa ta hannun kungiyar yakin neman zabensa, Tinubu ya ce an bude taron ne ga kowa, ciki harda malaman addini, jaridar Vanguard ta rahoto.

Daraktan yada muradu na kungiyar ta TCO, Bayo Onanuga ya zargi yan adawa da shiga lamarin don kai hare-hare mara amfani kan APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel