2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

2023: Kungiyar Kirista Ta Watsa Wa CAN Kasa A Ido, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi

  • Wata kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya mai suna 'Christ Shiloh Ambassadors of Nigeria' ta ce ba laifi bane Tinubu ya zabi mataimaki musulmi
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Pastor Ade Odudola da sakatenta Pastor Felix Rawa
  • Kungiyar ta ce ba addini bane abin da ya dace a lura da shi wurin zaben shugabanni kuma ta ce ba dukkan kiristoci bane suka yarda da matsayar CAN a lamarin

Wata kungiya, mai suna 'Christ Shiloh Ambassadors of Nigeria', ta ce ba laifi bane domin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya zabi musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023, rahoton The Punch.

Shettima Da Tinubu
2023: Kungiyar Kirista Ta Soki CAN, Ta Ce Ba Laifi Bane Tinubu Ya Zabi Mataimaki Musulmi. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Ba Zamu yi APC a zabe 2023 ba: Kiristocin Jihohin Arewa 19 Sun Jaddada

Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas, ya zabi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa. Sassa da dama na kasar sun nuna rashin jin dadinsu game da zabin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Pastor Ade Odudola da sakataren ta, Pasto Felix Rawa, suka fitar bayan babban taronsu da suka raba wa manema labarai, kungiyar ta ce ba addinin bane ya kamata ya zama abin dubawa wurin zaben shugabanni a 2023.

Kungiyar addinin ta roki kiristoci su goyi bayan tikitin musulmi da musulmi na Tinubu da Shettima, tana jadada cewa "demokradiyya batu ne na rinjaye kuma idan ana son nasara, dole a yi lissafi."

Kungiyar ta dage cewa ba dukkan kiristoci bane ke goyon bayan matsayar CAN kan tikitin musulmi da musulmi.

Sakon ya ce, "Ba dukkan kiristoci ne suke mambobin CAN ba kuma ba dukkan mambobin CAN bane ke goyon bayan abin da shugabannin ke yi a yanzu."

Kara karanta wannan

2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

A wani rahoton, Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, SGF, ya ce za a yaki tikitin musulmi da musulmi na jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023 da addu'a.

Lawal ya bayyana hakan ne yayin wani taro na shugabannin Kiristan Arewa da aka yi a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, ya zabi, Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, wanda shima musulmi ne a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel