Wanda Ya Nemi mulki a APC Ya Ki Yarda da Bola Tinubu, Ya Ayyana ‘Dan takararsa

Wanda Ya Nemi mulki a APC Ya Ki Yarda da Bola Tinubu, Ya Ayyana ‘Dan takararsa

  • Dr. SKC Ogbonnia ya fitar da jawabi, ya barrantar da kansa daga goyon bayan Bola Tinubu a 2023
  • Duk da yana ‘Dan jam’iyyar APC, Dr. SKC Ogbonnia yace Peter Obi zai marawa baya a Najeriya
  • Tsohon ‘Dan Takaran Shugaban Kasar ya kawo dalilan kin marawa Tinubu baya ya karbi mulki

Abuja - Tsohon ‘dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, SKC Ogbonnia ya shaidawa Duniya cewa zai yi doya da manja a zaben 2023.

Vanguard ta rahoto Dr. SKC Ogbonnia yana cewa bai goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu ya zama shugaban Najeriya a 2023, ya kuma ce yana tare da Peter Obi.

SKC Ogbonnia ya bayyana mubaya’arsa ga ‘dan takaran jam’iyyar Labor Party, yake cewa lokaci ya yi da duk za a hada kai da Peter Obi domin ya karbi shugabanci.

Kara karanta wannan

Tsintsiya ta tsinke a Borno: Dan a mutun Tinubu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Kamar yadda labarin ya zo a Nairaland, Dr. Ogbonnia yace bai sauya-sheka daga APC ba, zai cigaba da zama ‘dan jam’iyya, amma bai goyon bayan takarar Tinubu.

Amma ina nan a APC - Ogbonnia

“Duk da zan cigaba da zama ‘dan jam’iyyar APC, amma bazan taba goyon bayan ‘dan takaranta a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Dalilina na marawa ‘dan takarar jam’iyyar hamayya bai zo mani da sauki ba. Amma lokaci ya yi da dole za a ce: ‘abin ya isa haka nan.’”

- Dr. SKC Ogbonnia

'Yan Bola Tinubu
Magoya bayan Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Lamarin Tinubu sai Allah kawai

A jawabin da ya fitar a ranar Litinin wanda ya shigo hannun ‘yan jarida, Ogbonnia yace dalilinsa na kin bin Tinubu shi ne babu wanda ya san gaskiyar lamarinsa.

“Komai game da mutumin nan a boye yake – Daga sunansa, inda ya fito, makarantun da ya halarta, takardun shaidarsa, zamansa a Amurka, da dukiyarsa.

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya yi Magana Yayin da Jita-jitar Tunbuke shi ke yin Karfi a Majalisa

Ba a maganar sanin ainihin abin da ya sa yake neman shugabanci, baya ga gadarar cewa lokacinsa ne da yanzu zai mulki Najeriya." - Dr. SKC Ogbonnia

An rahoto jigon na APC yana cewa baya ga nuku-nuku game da zahirinsa, Tinubu bai da adalci, gaskiya, da kishin kasa, kuma bai da cikakken koshin lafiya.

Bugu da kari, Ogbonnia ya fito yana cewa bai dace gwamnatin APC ta cigaba da mulki ba, musamman ganin yadda aka hana kowa tikiti, aka tsaida tsoho.

‘Dan siyasar yake cewa ya bi sahun sauran talakawa da suke tare da Peter Obi a zabe mai zuwa na 2023, yace Obi mutum ne mara kabilanci da zai kawo gyara.

Babu mu, babu APC - CAN

Ku na da labari Sakataren kungiyar ta CAN, Sunday Oibe ya sake nuna cewa Kiristocin da ke Arewacin Najeriya ba su marawa Jam’iyyar APC baya a 2023 ba.

Sunday Oibe yana ganin ba Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima tutar APC da aka yi, ya nuna Jam’iyyar mai mulki ta maida Kiristoci saniyar ware a kasar nan.

Kara karanta wannan

A jini na take: El-Rufai ya ce mutuwa ce kadai za ta raba shi jam'iyyar APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel