Sauya sheka: Ta karewa APC a Borno yayin da Dan a Mutun Tinubu ya koma PDP

Sauya sheka: Ta karewa APC a Borno yayin da Dan a Mutun Tinubu ya koma PDP

  • Zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa na kara daukar sabon salo yayin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen ganin nasu ne ya gaji Buhari
  • A sansanin jam’iyyar APC mai mulki an samu tasgaro, an samu jiga-jigai da dama da ke ta sauya sheka cikin ‘yan makwannin da suka gabata
  • Daya daga cikinsu na baya-bayan nan shi ne Honorabul Abdu Musa Msheliza, tsohon dan majalisar da ya bar jam’iyyar APC zuwa babbar abokiyar hamayyar sa ta PDP

Jihar Borno - An kuma, mai yiwuwa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya sake fuskantar koma baya a jirgin yakin neman zabensa biyo bayan ficewar daya daga cikin abokan tafiyarsa.

Hon. Abdu Musa Msheliza, tsohon dan majalisar wakilai kuma mamba a kungiyar goyon bayan Tinubu a jihar Borno ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Elrufai Ya Ce APC ta Riga Ta Nada Darakata Janar Na Kamfen Din Takarar Tinubu Da Shettima

Yadda jigon APC ya koma PDP a Borno
Sauya sheka: Ta karewa APC a Borno yayin da Dan a Mutun Tinubu ya koma PDP | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A cewar rahoton, Msheliza ya bayyana cewa, ficewar sa daga APC ya samo asali ne daga yana son a samar da yanayi da za kawo yi adalci, daidaito da kuma shawarwarin a tafiya da harkokin siyasa.

Dalilin da ya sa na bar APC, Msheliza ya magantu

Ya bayyana cewa ba zai kasance a inuwar siyasar da inda mutum zai zabo wa jama’a da hannunsa wanda yake so a madadin ba su zabin kawo shugaban da suke so.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai ya yi wa shugabannin jam’iyyar PDP da daukacin ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar Borno alkawarin cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ya marawa jam’iyyar baya a kowane fanni domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaben 2023.

Msheliza ya bukaci al’ummar jihar Borno da su tsaya tsayin daka domin kada kuri’unsu a zabukan da ke tafe.

Kara karanta wannan

A jini na take: El-Rufai ya ce mutuwa ce kadai za ta raba shi jam'iyyar APC

Ya bukace su da kada su yi watsi da duk wani tsarin zabe, su kasance masu shiga a dama dasu kana su taka rawar gani a zabukan.

Gwamna El-Rufai: Zan Tabbata a APC Daga Yanzu Har zuwa Mutuwa ta

A wani labarin, gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa yana daya daga cikin mutane 37 da suka daura tsintsiyar jam’iyyar APC tun farko don haka ya dauki jam’iyyar a matsayin daya daga cikin ‘ya’yansa, rahoton Leadership.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta kai tsaye a gidajen rediyon Kaduna a daren Laraba, ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa yana shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kan batun Tinubu da Shettima.

El-Rufai ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC har zuwa karshen rayuwarsa, inda ya kara da cewa ‘’idan na bar APC, to na bar siyasa gaba daya’’.

Asali: Legit.ng

Online view pixel