Ba Zamu yi APC a zabe 2023 ba: Kiristocin Jihohin Arewa 19 Sun Jaddada

Ba Zamu yi APC a zabe 2023 ba: Kiristocin Jihohin Arewa 19 Sun Jaddada

  • Kungiyar kiristoci na CAN na reshen Arewacin Najeriya sun barranta daga goyon bayan APC
  • Sakataren CAN, Sunday Oibe ya bayyana cewa ba su tare da Bola Tinubu/Kashim Shettima a 2023
  • Oibe ya yi kira ga shugaban kasa da ‘Yan siyasa, sannan ya taya sabon shugaban CAN murna

Kaduna - Kungiyar kiristocin Najeriya watau CAN na reshen Arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa ba su goyon bayan APC a zaben shugaban kasa.

Sakataren kungiyar ta CAN, Sunday Oibe ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a karshen makon da ya gabata, Channels TV ta kawo wannan labari.

Sunday Oibe ya jaddada matsayar kungiyar Kiristan saboda matsayar da jam’iyyar APC ta dauka na tsaida Musulmi da Musulmi a zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

A Dena Kawo Addini Cikin Siyasa, In Ji Lalong, Shugaban Yakin Neman Zaben Tinubu

“Mu na tabbatar da matsayinmu a kan batun tikitin Musulmi da Musulmi a kasa mai tarin kabilu da addinai irin Najeriya.
Musamman idan aka yi la’akari da cewa ba a taba samun lokacin da aka raba kai ta fuskar addini da kabilanci irin haka ba."

- Sunday Oibe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace Oibe ya yi kira ga ‘yan siyasa da jam’iyyu suyi hattara da masu lallabawa da dare suna neman ganawa da su, da sunan malaman addini.

Kiristoci
Wasu Fastoci a Fadar Shugaban kasa Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Sakataren kungiyar yace CAN ba za ta zauna da wani ‘dan siyasa ko jam’iyyar siyasa a boye ba.

Matsalar tsaro a yau

Amma duk da haka, shugaban kiristocin yace za su bar kofa a bude ga duk wani mai sha’awar zama da su domin kawo shawarar yadda za a gyara Najeriya.

A jawabin na sa, Oibe ya yi tir da yadda tsaro ya tabarbare, ya yi kira na musamman ga shugaba Muhammadu Buhari ya tashi-tsaye wajen kare mutanensa.

Kara karanta wannan

Ba za ta sabu ba: Kungiyar kiristoci ta fara yaki da ci da addini, za ta ba da katin shaida ga malamai

“’Yan ta’adda sun yi wa Najeriya zobe, suna tafka ta’adi a kan al’umma, suna gurgunta tattalin arziki da rayuwar mutanen kasa.
Musamman a jihohi kamarsu; Kaduna, Katsina, Zamfara, Niger, Benue, Plateau, Taraba, Kebbi, Sokoto, da Abuja – birnin tarayya.

- Sunday Oibe

Mubaya'a ga sabon shugaban CAN

Kamar yadda jaridar nan ta Punch ta kawo rahoto, CAN ta yi kira ga shugaban kasa da majalisar tarayya suyi maza su dauki matakan da suka dace.

A karshe, a madadin daukacin Kiristocin da ke jihohi 19 na Arewa da birnin Abuja, Oibe ya taya Rabaren Daniel Oko murnar zama shugaban CAN.

An tasa Dogara, Babachir gaba

Mun samu rahoto cewa rikicin da ake yi a jam’iyyar APC a game da tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a zaben 2023 ya jawo ana wasan tonon silili.

Ana zargin Babachir Lawal da Yakubu Dogara sun yi wa Bola Tinubu aiki ne a APC, suka hana Yemi Osinbajo samun takara, sai yanzu suke yin nadama.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun harbi shugaban 'yan sanda, sun kashe jami'in kariyarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel