An Riga An Zabi Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A APC, Inji El-Rufai

An Riga An Zabi Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A APC, Inji El-Rufai

  • Gwamnan Jihar Kaduna ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta riga ta nada daraka janar na yakin neman zaben shugaban kasa a 2023
  • Elrufai ya ce za a sanar da Buhari da Abdullahi Adamu wanda aka nada Darakata Janar kamfen din Tinubu kafin a fitar da sunan sa
  • Wadanda suka halarci taron sun hada da Oshiomhole da sakataren jam’iyyar APC na kasa, Iyiola Omisore

Jihar Legas - Gabanin zaben 2023, an zabi babban darakta a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Rahoton Channels TV

Wannan shine jawabin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya bayyanawa manema labarai a ranar Litinin bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, da abokin takararsa Kashim Shettima, a Legas.

Kara karanta wannan

Tsintsiya ta tsinke a Borno: Dan a mutun Tinubu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Ya ce ana tattaunawa kan wasu mukamai a majalisar, inda ya ce za a sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu kafin a fitar da sanarwar.

elrufai
An Riga An Zabi Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A APC, Inji El-Rufai FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Elrufai ya ce zai ba da rahoto akan wani aiki da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da abokin takararsa suka ba su don fara tattaunawa mai zurfi da samar da tsarin kwamitin yakin neman zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ko da yake akwai wasu rahotanni da ke cewa an nada tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole a matsayin darakta-janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, amma ya musanta hakan.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Oshiomhole da sakataren jam’iyyar APC na kasa, Iyiola Omisore.

Baba-Ahmed Ya Bayyana Matsayar Peter Obi A Kan Kungiyar IPOB Ta Nnamdi Kanu

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu : Tinubu Ya Tafka Kuskure Da Ya Dauki Abokin Takara Musulmi – Yakubu Dogara

A wani labari kuma, Kungiyar kiristocin Najeriya watau CAN na reshen Arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa ba su goyon bayan APC a zaben shugaban kasa.

Sakataren kungiyar ta CAN, Sunday Oibe ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a karshen makon da ya gabata, Channels TV ta kawo wannan labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel