Ana Tonon Silili, An Fara Fadan ‘Yan APC da Suka Hana Osinbajo Samun Takaran 2023

Ana Tonon Silili, An Fara Fadan ‘Yan APC da Suka Hana Osinbajo Samun Takaran 2023

  • Ana zargin Babachir David Lawal da Yakubu Dogara da kin goyon bayan takarar Yemi Osinbajo
  • Da Yemi Osinbajo ya nemi tikitin APC, wadannan ‘Yan siyasa ba su ba shi goyon baya a APC ba
  • A yau Lawal da Dogara suna rikici saboda Bola Tinubu ya ki daukar Kirista ya yi masa Mataimaki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Lagos - Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar APC suna ta maidawa junansu martani a dalilin korafin da ake yi wa Bola Tinubu na dauko Kashim Shettima.

Lamarin ya kai an bayyana cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya yi wa Bola Tinubu aiki a zaben takaran shugaban kasa.

Haka zalika an fahimci tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya taimakawa Tinubu ne wajen samun tikiti a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Mayar da Kiristan Arewa saniyar ware: Babachir da Yakubu Dogara Sun Kai Wa Wike Ziyara A Jihar Ribas

Wadannan jagororin APC na Arewacin Najeriya ba su marawa Farfesa Yemi Osinbajo baya a zaben fitar da gwanin da aka shirya a watan Mayun 2022 ba.

Bayan tsaida Tinubu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa, sai ya yi watsi da kiristocin Arewa, ya nemi Kashim Shettima ya zama abokin takararsa.

Da alamun hakan bai yi wa musamman kiristocin Arewa da ke jam’iyyar APC mai mulki dadi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An fara fasa-kwai

Wani mai suna Otunba Akintola Akinwumi Peter ya fallasa Injiniya Babachir Lawal da Hon. Dogara. Joe Igbokwe ya dauko maganarsa a shafin Facebook.

Otunba Akintola Peter yake cewa a lokacin zaben tsaida gwani, ‘yan siyasar ba su yi la’akari da addini ba, saboda suna sa ran Tinubu zai dauke su a APC.

Babachir Lawal da Yakubu Dogara
Babachir Lawal da Yakubu Dogara Hoto: @joeigbokwe.igbokwe
Asali: Facebook

Maganar da Otunba Peter ya yi

Kara karanta wannan

Kiristocin Jagororin APC 4 da Suka Juyawa Tinubu Baya kan Takarar Musulmi-Musulmi

“Za kayi tunanin wadannan mutane suna yi wa addinin Kirista aiki ne. Sam! Suna goyon bayan kansu da kuma san ransu ne kurum.
Babachir da Dogara sun yi wa Tinubu aiki ne a zaben fitar da ‘dan takaran APC, suka yaki da Fasto Yemi Osinbajo, ‘danuwansu kirista.
Yanzu ba su samu tikitin shugaban kasa ba, sai suka yi wuf suka tuna da batun addinin Kirista. Ni Kirista ne, amma ba ni son munafunci.”

Su wanene ke yakar Tinubu a yau?

A halin yanzu, kun samu labari cewa Kiristoci musamman na Arewacin Najeriya suna nuna rashin goyon bayan tikitin Tinubu da Kashim Shettima.

Sanata Elisha Abbo bai boye fushinsa kan yadda Bola Tinubu ya dauko Musulmi ba, shi ma Daniel Bwala ya fice daga jam'iyyar APC da jin wannan labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel