Babachir David Lawan Da Dogara Sun Kai Wa Wike Ziyara A Jihar Ribas

Babachir David Lawan Da Dogara Sun Kai Wa Wike Ziyara A Jihar Ribas

  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawan da tsohon kakakin majalisar wakilai sun kai wai Wike ziyara a Fatakwal
  • Lawan da Yakubu Doagara sun lashi takobin adawa da tikitin tsayawa takarar Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC mai mulki
  • Yakubu Dogara ya bayyana cewa daukar Kashim Shettima a matsayin abokin takara da Tinubu yayi Tafka kuskure ne

Jihar Ribas - Babachir David Lawan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, da Yakubu Dogara tsohon kakakin majalisar wakilai , sun kai wa gwamnan jihar Ribas ziyara a gidan sa dake Fatakwal. Rahoton LEADERSHIP

Babachir David Lawal da Yakubu Dogara jiga-jigan yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne yayin da Gwamna Nyesom Wike kuma jigo ne jam’iyyar PDP.

Ziyarar na zuwa rana daya bayan sun gudanar taron Manyan Kiristocin Arewacin Najeriya da a birnin Abuja a ranar Juma'a, inda suka dau alwashin adawa da tikitin takarar Musulmi da Musulmi da jam’iyyar APC mai mulki ta yi.

Kara karanta wannan

Kiristocin Jagororin APC 4 da Suka Juyawa Tinubu Baya kan Takarar Musulmi-Musulmi

Babachir
Babachir David Lawan Da Dogara Sun Kai Wa Wike Ziyara A Jihar Ribas FOTO LEADERSHIP
Asali: UGC

Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan ganawar sirri da yayi da Dogara da Babachir, cewa shugabannin biyu sun kawo mishi ziyarar dan uwantaka ne kawai da neman gyara da hadin kan yan Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.NG Ta rawaito labarin sakamakon taron da manyan kristocin Arewa suka gudanar a ranar Juma’a 29 ga watan Yuni a Abuja inda tsohon kakakin majalisar wajilar, Yakubu Dogara ya bayyana cewa daukar Kashim Shettima a matsayin abokin takara da Tinubu yayi Tafka kuskure ne

EFCC Ta Yiwa Yan Kasuwar Canjin Dala Dirar Mikiya A Abuja

A wani labari kuma, Jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawan Najeriya EFCC sun kai wa yan kasuwar canji da ke unguwar Wuse Zone 4 a Abuja samame da nufin kama masu boye dala, kamar yadda Jaridar BBC Ta rawaito.

Rahotanni sun ce EFCC ta dauki matakin kaiwa 'yan kasuwar canji samame ne saboda saya da boye dalar Amurka da suke yi, wanda yana cikin abin dake sa darajar naira na kara faduwa a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel