Da Dumi-Dumi: Kungiyar CAN Ta Nesanta Kanta Da Bishop-Bishop Da Suka Hallarci Kaddamar Da Shettima

Da Dumi-Dumi: Kungiyar CAN Ta Nesanta Kanta Da Bishop-Bishop Da Suka Hallarci Kaddamar Da Shettima

  • Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, ta nesanta kanta da Bishop-Bishop din da suka hallarci taron kaddamar da Kashim Shettima
  • Rabaran Jospeh Hayab, shugaban CAN na Kaduna kuma mataimakin shugaban kungiyar na kasa ya ce wasan kwaikwayo ne Tinubu da APC ta yi
  • Kungiyar ta CAN ta shawarci tawagar ta dan takarar shugaban kasar na APC, Tinubu, ya daure ya yi abin da ya dace na adalci ya dena dirama

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN, a ranar Laraba ta nesanta kanta daga Bishop-Bishop da suka hallarci kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima, suna cewa don wata manufar kashin kansu suka tafi.

Bishop da suka hallarci kaddamar da Kashim Shettima.
Da Dumi-Dumi: Kungiyar CAN Ta Nesanta Kanta Da Bishop-Bishop Da Suka Hallarci Kaddamar Da Shettima. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Kungiyar ta ce duk da cewa dan takarar shugaban kasar na APC, Bola Ahmed Tinubu, yana da ikon "daukar hayar makanikai da wasu masu sana'ar hannu ya dinka musu riguna amma hakan ba zai canja bukatar da ke akwai na yin adalci ba."

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

Mataimakin shugaban CAN na (Jihohi 19 da Abuja) da shugabanta a Kaduna, Rabaran Jospeh Hayab ne ya furta hakan a wani hira da yayi da manema labarai a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Mutanen da muka gani a taron kaddamar da Shettima da aka gabatar a matsayin Bishops mutane ne da ba su samu isashen lokacin koyon saka tufafin Bishop ba. Duba hoton sosai za ka ga wani fim ne na Nollywood.
"CAN tana mamakin wannan gaggawar. Da farko labari da ya fito da aka ce daga shugaban CAN na Borno amma aka karyata. Na biyu akwai wani karyar cewa BAT (Bola Ahmed Tinubu) da abokin takararsa suna hanya don ganawa da shugaban CAN da dare. Taron da ba gaskiya bane domin shugaban CAN yana Alabama, Amurka, yana hallarton taron Baptist World Alliance inda shine mataimakin shugaba."

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

A jawabin da ya fara, Bishop din ya cigaba da cewa:

"Wani labarin karyar shine cewa Papa Adeboye ya gana da su daga bisani RCCG ta karyata. Idan kirista ba su da muhimmanci me yasa ake ta wannan zarin?
"BAT yana da damar daukan hayan makanikai da sauran masu sana'ar hannu ya dinka musu kaya. Wannan yunkurin dai na siyasa ne amma ba zai canja bukatar adalci da CAN ke kira a yi ba.
"CAN ta lura cewa muna demokradiyya ne, don haka babu bukatar yin wani abin ban dariya ko yaudara don cimma wata manufa domin ba zai haifar da da mai ido ba. Tawagar BAT ta yi abin da ya dace ta dena diraman nan."

Tsoron Tinubu Da Shettima Yasa Yan Adawa Ke Babatu Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Kungiya

A bangare guda, Mallam Abdulazeez Yinka Oniyagi, Jagoran Kungiyar Goyon Bayan Tinubu (TSO) ya ce tsoron Tinubu da Shettima ne yasa masu adawa ke daukan nauyin masu dumama siyasa kan batun tikitin musulmi da musulmi.

Hakan ne zuwa ne a lokacin da Direkta Janar na TSO, Hon Aminu Suleiman ya ce kungiyar za ta koma ta yi nazari don kaucewa 'kuskuren' da jam'iyyar ta yi a Jihar Osun ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel