Yanzu-Yanzu: Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima

Yanzu-Yanzu: Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima

  • Gwamnonin APC sun ce sun gamsu da zaben Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu
  • Shugaban kungiyar gwamnonin APC Abubakar Bagudu ne ya bayyana matsayin gwamnonin bayan sun gana da shugaba Buhari
  • Hope Uzodimma, gwamnan jihar Imo, ya kuma yi tsokaci kan yadda Shettima ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC

Daura, jihar Katsina – Gwamnonin jam’iyyar APC tara sun yi ganawar sirri ta sa’a daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli.

A karshen taron, gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar maaimakin shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, inji rahoton jaridar Punch.

Gwamnonin APC sun goyi bayan takarar Tinubu da Shettima
Yanzu-Yanzu: Bayan ganawa da Buhari, gwamnonin APC sun fadi matsayarsu kan takarar Tinubu da Shettima | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa gwamnonin sun kuma ce sun amince da hadakar Tinubu da Shettima domin tabbatar da nasarar jam’iyyar mai mulki a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Naka sai naka: Shugaban kungiyar CAN a Borno ya goyi bayan takarar Shettima

An jiyo shugaban kungiyar gwamnonin na APC Abubakar Bagudu yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun yi matukar mamakin lokacin da Asiwaju Ahmed Tinubu ya bayyana a Daura ranar Lahadi cewa Sanata Kashim Ibrahim Shettima ne dan takarar mataimakin shugaban kasa.
“Mun yi farin ciki da cewa ba karamin mutum ba ne Sanata Shettima da aka bayyana dan takarar mataimakin shugaban kasa. Babu shakka, Sanata Shettima zai cika kyawawan manufofin Asiwaju Tinubu.
"Mun yi matukar farin ciki da zabin, su biyun za su kara kaimi, kuma za su karfafa nasarorin da shugaban kasa ya samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata."

Bagudu ya kara da cewa ziyarar da suka kai Daura sun kai ta ne domin taya shugaban kasar murnar Sallah.

Yadda aka zabo Shettima, inji gwamna Uzodimma

A bangare guda, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, shi ma ya ce zabar Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa shawara ce ta dukkanin gwamnonin APC.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Kwankwaso ya gamsu da hadin Tinubu da Shettima

Ya kara da cewa dukkan gwamnonin za su yi aiki tukuru domin ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben 2023.

A kalamansa:

“Zaben Sanata Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa shawara ce ta gama-gari. Za mu yi aiki tukuru don ganin mun samu nasara a dukkan jihohinmu”.

Kwankwaso: Idan na rasa kujerar Buhari, kowa ma ya rasa, amma Tinubu ya samu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya ce zai marawa takwaransa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu baya, idan ya ga ba zai ka ga gaci ba a zaben 2023.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi a gidan talabijin na Arise a daren Lahadi.

Tsohon gwamnan na Kano ya yi magana ne biyo bayan sanarwar da Tinubu ya yi na zabi Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel