'Dan majalisa da dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jiha ɗaya

'Dan majalisa da dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jiha ɗaya

  • Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ta shiga babban rikici a jihar Oyo yayin da dubbannin mambobinta suka rungumi APC
  • Ɗan majalisar tarayya, Muraina Ajibola, ya jagoranci mambobi sama da 18,000 sun koma APC daga PDP
  • Shugaban APC reshen jihar ya ce zasu yi duk me yuwuwa wajen ɗinke ɓarakar cikin gida don kwace mulkin jihar daga hannun PDP

Oyo - Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ibarapa Central/Ibarapa a majalisar tarayya, Muraina Ajibola, ya jagoranci dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a jihar Oyo.

Daily Trust ta ruwaito cewa masu sauya sheƙan sun sami kyakkyawan tarba daga shugaban APC reshen jihar Oyo, Isaac Omodewu, ɗan takarar sanatan Oyo ta kudu, Akogun Sarafadeen Alli, da wasu jagororin jam'iyya a ƙarshen makon nan.

Kara karanta wannan

Danbarwa ta ɓarke a majalisar dokokin jiha a arewa, mambobi 22 sun ɓalle, sun nemi kakaki ya yi murabus

Honorabul Ajinbola ya bayyana cewa a iya bayanan da ya tattara aƙalla mutum 18,000 ne suka biyo shi zuwa sabuwar jam'iyyarsa APC daga PDP.

Tambarin APC da PDP.
'Dan majalisa da dubbannin mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC a jiha ɗaya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Matakin da APC ke bi don ɗinke barakarta

Da yake jawabi a wurin taron tarban mutanen wanda ya gudana a garin Igangan, ƙaramar hukumar Ibarapa ta arewa, shugaban APC a jihar ya ce a matsayin jagoran jam'iyya na jiha ya jima ya na lallashin mambobin da suka fusata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isaac Omodewu ya ƙara da cewa kokarin da yake da lallaɓa mambobin APC da suka fusata ya fara haifar da ɗa mai ido, jam'iyya zata dunƙule wuri guda.

Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu lallasa PDP - Omedewu

Omedewu ya kuma tarbi dubbanin masu sauya sheƙan, inda ya ce lokaci ya yi da zasu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen kawar da PDP mai mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

A jawabinsa ya ce:

"Mun zo nan ne don tabbatar da haɗa kan mutanen mu. Wannan dandazon mutane ne da suka dawo cikin mu daga PDP. Ba zamu yi ƙasa a guiwa ba muna rokon 'ya'yan jam'iyyar mu su zauna a gidan su."
"Ba su da wani abu da zasu iya yi idan suka fita daga jam'iyya a lokacin da muke hana idanuwan mu bacci domin dawo da gidan gwamnatin Agodi hannun mu a zaɓen 2023."
"Ga dukkan masu tunanin sauya sheƙa a cikin su, su tuna babu wurin da ya fi gida, su cigaba a zama a gidansu. A matsayin shugaban jam'iyya ba zan gajiya ba wajen rarrashin su zauna a APC."

A wani labarin na daban kuma Jerin gwanon motocin gwamnan arewa sun yi hatsari a babbam birnin tarayya Abuja

Wani hatsari ya rutsa da Jerin gwanon motocin gwamnan jihar Benuwai da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Da alama guguwar sauya sheƙa ba ta lafa ba a APC, wani ɗan takarar gwamna ya fice daga jam'iyyar

Wata sanarwa da gwamnatin jihar Benuwai ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da motocin suke kan hanyar komawa baya kai gwamna Filin Jirgi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel