Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi, mambobi 22 sun buƙaci kakaki ya yi murabus

Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi, mambobi 22 sun buƙaci kakaki ya yi murabus

  • Rikicin shugabanci ya kunno kai a majalisar dokokin jihar Bauchi yayin da mambobi 22 suka nemi duk me rike da ofishi ya yi murabus
  • Shugaban mambobin 22 kuma mataimakin shugban masu rinjaye ya ce su aje aiki ko kuma su tsige su kowane lokaci ɗaga yanzu
  • Kakakin majalisar, Abubakar Suleiman, bai daɗe da sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP ba

Bauchi - Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi kan shugabanci bayan buƙarar mambobin majalisa 22, waɗan da suka kaɗa kuri'ar rashin kwarin guiwa kan kakaki da sauran shugabannin majalisa saboda gazawa.

Punch ta ruwaito cewa kakakin majalisar jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, shi ne shugaban majalisar kakakin majalisun jihohi Najeriya.

Idam baku manta ba, ba da jimawa ba Suleiman ya sauya sheƙa daga jam'iyyar APC da aka saɓen shi ƙarkashinta zuwa PDP, hakan ya sa mambobin APC suka koma 16 yayin da PDP ke da 15.

Kara karanta wannan

Zamfara: Matar shugaban ma'aikata da aka sace ta haihu a sansanin 'yan bindiga, ta kira shi a waya

Majalisar dokokin jihar Bauchi.
Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi, mambobi 22 sun buƙaci kakaki ya yi murabus Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Abun sha'awar shi ne, mambobi 22 da suka kaɗa kuri'ar rashin kwarin guiwa kan kakakin da sauran shugabanni, sun haɗa mambobin PDP 7 da kuma na APC 15.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakin shugaban masu rinjaye, Baballe Dambam (APC), mai wakiltar mazaɓar Dambam/Dagauda/Jalam, wanda ke jagorantar mambobin da suka ɓalle ya ce jagorancin majalisa ya gaza ta ko ina kan mambobi.

Saboda haka suka yi kira ga shugabannnin su yi murabus dan ƙashin kan su ko kuma su tsige su kowane lokaci daga yanzu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jagoran mambobin 22 da sukan ɓalle, wanda ya yi hira da yan jarida bayan wani taro da suka yi a zauren majalisa, ya ce:

"Bayan taron da muka yi yau Jumu'a 1 ga watan Yuli, 2022, mambobi 22 na majalisar dokoki sun kaɗa kuri'ar rashin kwarin guiwa kan jagororin gidan daga yau."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sako ma'aikatan lafiya, sun maida miliyoyin kuɗin da aka kai musu a Zamfara

"Mu ɗauka daga yau babu shugabanci a majalisar Bauchi, ina daga cikin shugabanni, amma wannan shi ne lokacin da ya dace kuma dole mu ɗauki mataki."
"Muna kira ga shugabannin majalisar Bauchi cewa su gaggauta miƙa takardun murabus ɗinsu ga magatakardan majalisa. Hakan zai ba gida damar zaɓen sabbin shugabanni."

A wani labarin kuma Wata matar aure ta sa yan bindiga sun yi garkuwa da Mijinta kan wani saɓani tsakanin su

Asirin wata matar aure a Kwara ya tonu yayin da ta ƙulla yin garkuwa da mijinta kan wani sabani da ya shiga tsakanin su.

Matar mai suna Delu Ali, ta amsa laifinta, ta ce ta yi haka saboda rikicinta da shi game da raba wasu dabbobi a tsakanin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel