Da Ɗumi-Ɗumi: Tawagar motocin gwamnan Arewa ta yi haɗari a Abuja

Da Ɗumi-Ɗumi: Tawagar motocin gwamnan Arewa ta yi haɗari a Abuja

  • Wani hatsari ya rutsa da Jerin gwanon motocin gwamnan jihar Benuwai da ke arewa ta tsakiya a Najeriya ranar Lahadi
  • Wata sanarwa da gwamnatin jihar Benuwai ta fitar ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da motocin suke kan hanyar komawa baya kai gwamna Filin Jirgi
  • Babu wanda ya mutu a hatsarin wanda wata motar Golf ta ci karo da ɗaya daga cikin motocin da suka wa gwamna rakiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jerin gwanon motocin gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, a ranar Lahadi, wani hatsari ya rutsa da su a babban birnin tarayya Abuja.

Leadership ta rahoto cewa tawagar motocin gwamnan na kan hanyarsu ta komawa Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai bayan sun raka gwamnan filin jirgi don ya kama hanyar zuwa Birtaniya yayin da hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.
Da Ɗumi-Ɗumi: Tawagar motocin gwamnan Arewa ta yi haɗari a Abuja Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa wata Motar Golf ce ta yi taho mu gama da ɗaya daga cikin motocin jami'an tsaro da ke cikin jerin gwanon motocin gwamna Ortom.

A wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan ta fannin yaɗa labarai, Terver Akase, ya fitar ya bayyana cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa sanadiyyar haɗarin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda abun ya faru

Ya ce lamarin ya auku ne lokacin jerin gwanon motocin suke kan hanyar koma wa jihar Benuwai bayan raka mai girma gwamna filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A kan hanyar ne ɗaya daga cikin jerin motocin ta yi karo da wata motar Golf a kusa da gadar Nyanya a birnin tarayya, a cewarsa.

Sanarwan ta ce:

"Mun sami kiran waya da dama daga yan Najeriya masu ƙaunar mu game da haɗarin da ya auku a kusa da Gadar Karu da ke yankin Nyanya a babban birnin tarayya Abuja."

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

"Muna ƙara godiya ga Allah ba bu wanda ya rasa rayuwarsa a haɗarin, tuni gwamna Samuel Ortom ya sauka a Birtaniya lafiya. Mun yaba da jin daɗin nuna ƙauna da kulawa daga mutanen Benuwai da yan Najeriya."

A wani labarin kuma Rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Bauchi, mambobi 22 sun buƙaci kakaki ya yi murabus

Rikicin shugabanci ya kunno kai a majalisar dokokin jihar Bauchi yayin da mambobi 22 suka nemi duk me rike da ofishi ya yi murabus.

Shugaban mambobin 22 kuma mataimakin shugban masu rinj a ye ya ce su aje aiki ko kuma su tsige su kowane lokaci ɗaga yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel