Kafin 2023: Tashin hankali a APCn Katsina, dubban mambobi sun fece zuwa PDP

Kafin 2023: Tashin hankali a APCn Katsina, dubban mambobi sun fece zuwa PDP

  • Jam'iyyar PDP ta samu sabbin mambobi a jiha Asabar yayin da 'yan APC da yawa suka yanke shawarar sauya sheka
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ke ci gaba da da shirye-shiryen babban zaben 2023 mai zuwa
  • A jawabansu, wadanda suka sauya shekan sun bayyana ainihin dalilin da yasa suka yanke shawarin barin APC

Matazu, Jihar Katsina - A ranar Asabar din da ta gabata ne jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta karbi jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki da dubban magoya bayansu.

Jigon jam’iyyar APC, Alhaji Ali Maikano Matazu, wanda tsohon darakta ne na NNPC, ya nemi tikitin APC a mazabar Matazu/Musawa na majalisar wakilai amma ya sha kaye saboda abin da ya kira “rashin adalci a jam’iyyar.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya katange ni daga yakin neman zabensa saboda na janye wa Osinbao - Dr Felix

Yadda 'yan APC suka barta suka koma PDP a Katsina
Kafin 2023: Ta karewa a APC a Katsina, dubbai sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Masu sauya shekar sun samu tarbar dan takarar gwamnan PDP a jihar, Sanata Yakubu Lado Danmarke tare da shugaban jam’iyyar na jiha Yusuf Salisu Majigiri da sauran shugabannin jam’iyyar a Matazu.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, Majigiri ya ce sama da ‘yan jam’iyyar APC 5,000 ne suka halarci taron na sauya sheka.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi ga dimbin jama’a a garin Matazu, Sanata Danmarke ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsa ta lashe zaben dukkanin kujerun kananan hukumomin da aka gudanar kwanan nan, amma jam’iyyar APC mai mulki ta murde lamarin.

Sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa a zabe mai zuwa, inda ya ce jam’iyyar PDP za ta samu nasara a jihar cikin sauki, yana mai kuma cewa yadda hukumar zabe ta kasa ta gudanar da zabukan baya-bayan nan, gaskiya za ta yi nasara akan karya.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Daga nan sai ya bukaci daukacin ‘yan jam’iyyar da magoya bayansa da su tabbatar da cewa katin zabensu na dindindin (PVCs) yana nan daram gabanin zaben.

A nasa jawabin, Alhaji Ali Maikano, wanda aka baiwa tikitin PDP don wakilcin mazabar, ya ce a baya suna APC amma ba abin da suke gani face rashin adalci, fatara, yunwa, garkuwa da mutane da kashe-kashe, shi ya sa suka yanke shawarar komawa PDP don nemo mafita.

2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

Akalla mambobin jam’iyyar PDP 10,000 ne aka bayyana cewa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Osun a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa, an yi wannan biki na sauya sheka ne a filin shakatawa na Nelson Mandela da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Legit.ng ta tattaro cewa Hon Wale Ojo, shugaban tsagin PDP na jihar, da Hon Albert Adeogun, dan takarar mataimakin gwamnan PDP a zaben 2018 a Osun, na daga cikin wadanda suka fice daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

PDP ta dakatar da shugabanta a wata jihar arewa, ta bayyana dalili mai karfi

Wasu fitattun sunayen da suka koma jam’iyyar APC mai mulki su ne tsohon dan majalisar wakilai; Ayodele Asalu (Asler), dan takarar majalisar wakilai a mazabar tarayya ta Ede da kuma Soji Ibikunle, kusan jam'iyyar.

Zaben 2023: APC za ta kaddamar da tashar yanar gizo da za ta sa a dama da matasa a siyasa

A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ba shirya wasa ba, domin ta shirya kaddamar da shafin yanar gizo domin hada kan matasa kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dayo Israel ya bayyana shirin ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni a Abuja.

Mista Israel ya bayyana cewa sabon shirin an yi shi ne domin tabbatar da damawa da matasa a harkokin siyasar jam'iyyar. Ya ce dandali ne da ake son amfani dashi wajen jawo hankalin matasa zuwa jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun dumfari kotu, su na so a hana Atiku, Tinubu da Obi tsayawa takara a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel