Tinubu ya daina kula ni bayan na janye wa Osinbajo - inji Dan takara

Tinubu ya daina kula ni bayan na janye wa Osinbajo - inji Dan takara

  • Dr Nicholas Felix, ya yi korafin cewa dan takarar jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya katange shi daga yakin neman zabensa a zaben 2023
  • Felix ya ce yana ganin Tinubu ya share ni saboda ya goyi bayan mataimakin shugaban kasa dan baya ra’ayin ra'ayin tikitin musulmi da musulmi
  • Felix ya bayyana goyon bayan sa ga mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo a zaben fiida gwani da jam’iyyar APC ta gudanar

Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress, Dr Nicholas Felix, ya yi korafin cewa dan takarar jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya katange shi daga yakin neman zabensa a zaben 2023 dake zuwa.

Korafin dan takarar wanda shine mai mafi karancin shekaru a jam’iyyar APC ya zo ne makonni uku bayan taron da aka yi a dandalin Eagle Square da ke Abuja, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Tinubu Zai Zabi Mataimakinsa Daga Cikinsu

Felix ya bayyana goyon bayan sa ga mataimakin shugabankasa, Yemi Osinbajo a zaben fiida gwani da jam’iyyar APC ta gudanar.

Vanguard
Tinubu ya daina kula ni bayan na janye wa Osinbajo - inji Dan takara
Asali: Original

Kafin ya janye daga takarar shugaban kasa ya marawa Osinbajo baya, Felix ya bayyana Osinbajo a matsayin ‘mutumin da ya fi dacewa da aikin’, kuma yana da yakinin cewa zai iya kawo gyara a kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya samu nasarar doke Osinbajo, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, da wasu ’yan takara goma sha daya a zaben.

Yace:

"Asiwaju bai kira ni ba. Haka kuma babu wani memba na tawagar yakin neman zabensa da ya kira ni. Nine dan takara daya tilo da Asiwaju bai kai wa ziyara ba. Ban san dalili ba. Watakila saboda na goyi bayan mataimakin shugaban kasa ne ko kuma dan bana ra'ayin tikitin musulmi da musulmi ba,"

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Barakar PDP ta ki dinkewa, Wike ya yi watsi da wanda Atiku ya tura kasar waje ayi sulhu

A wani labarin kuwa, a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, Nyesom Wike ya ki bada dama ya zauna da tsohon Ministan harkokin ‘yan sanda, Adamu Maina Waziri.

Wike wanda yana kasar Turkiyya, ya ki ba Adamu Waziri damar da za su zauna domin su tattauna, har a iya maganin rikicin da yake neman barkewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel