Kujerar Shugaban PDP na lilo bayan sabon rikicin da ya barke kan abokin takaran Atiku

Kujerar Shugaban PDP na lilo bayan sabon rikicin da ya barke kan abokin takaran Atiku

  • An soma yada jita-jita cewa an tunbuke Dr. Iyorchia Ayu daga matsayinsa na shugaban PDP na kasa
  • Rade-radin na nuna bayan sauke Dr. Iyorchia Ayu, har Amb. Umar Damagum ya maye gurbin na sa
  • Ayu yana na a kan kujerarsa, amma babu shakka akwai masu huro wuta lallai sai an yi waje da shi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nigeria - Rigimar da ta barke a jam’iyyar PDP bayan zaman Gwamna Ifeanyi Okowa ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na 2023 na kara rincabewa.

Rahoton da Daily Trust ta fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, ya nuna cewa lamarin ya kai ga ana kiran a sauke shugaban PDP, Dr. Iyorchia Ayu.

Masu neman a tunbuke shugaban jam’iyyar adawar na kasa, har sun soma yada jita-jitar an sauke shi. Tuni sakatariyar jam’iyyar PDP ta karyata labarin nan.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnonin APC sun zauna, sun yi shawarwari kan yankin da zai kawo abokin tafiyar Tinubu

Hadimin shugaban jam’iyyar na PDP, Simon Imobo-Tswam ya ce Iyorchia Ayu bai sauka daga kujerarsa, har Amb. Umar Damagum ya karbi matsayin ba.

Iyorchia Ayu ya tafi hutu ne

Wani jawabin da Debo Ologunagba ya fitar ya ce Ayu ya dauki hutun makonni biyu ne daga ranar 21 ga watan Yuni, kuma zai dawo bakin aiki a makon gobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun bakin shugaban jam’iyyar ta PDP ya yi kira ga musamman masu amfani da kafofin sada zumunta na zamani su daina biyewa jita-jita.

Bala Mohammed da Nyesom Wike
Kwamitin da ya gana da Nyesom Wike Hoto: @senbalamohammed
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewacin Najeriya, Amb. Umar Damagum yana rike da kujerar ne kafin Ayu ya dawo ofishinsa a ranar 6 ga watan Yul.

Gwamnonin PDP su na bore

Sabanin da aka samu a PDP ya fito fili wajen rantsar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan Osun, gwamnoni biyu suka iya halarta a cikin goma da aka kira.

Kara karanta wannan

PDP ta dakatar da shugabanta a wata jihar arewa, ta bayyana dalili mai karfi

Shugaban rikon kwarya na PDP, Amb. Umar Damagum ne wanda ya rantsar da kwamitin, ya kuma yi kira gare su da su yi kokarin karbe jihar daga hannun APC.

Gwamnonin jihohin da aka gani su ne shi Ifeanyi Okowa da Gwamnan Taraba, Darius Ishaku. Ragowar gwamnonin sun kauracewa gayyatar da aka yi masu.

Masu hasashe da fashin baki su na ganin wannan rikicin cikin gida ya taimaka wajen kawowa PDP cikas a zaben sabon gwamnan jihar Ekiti da APC ta yi nasara.

Dauko Okowa ya kawo rikici

Ku na da labari cewa wanda zai rike kujerar takarar Mataimakin Shugaban kasa ya zama abin rigima a PDP, na-kusa da Gwamna Nyesom Wike sun tada rigima.

Da yake magana a jiya, Atiku Abubakar ya nuna zai sasanta da Nyesom Wike da ire-irensa ta hanyar lalama domin ganin ya doke jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Tashin hankali a PDP yayin da mambobi 10,000 suka tsallake zuwa APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel