An samu mummunan yamutsi a PDP, rikici ya ki karewa kan abokin takarar Atiku Abubakar

An samu mummunan yamutsi a PDP, rikici ya ki karewa kan abokin takarar Atiku Abubakar

  • An ji Gwamna Samuel Ortom yana sukar Atiku Abubakar a kan kin tafiya da Nyesom Wike a PDP
  • Kamar Ayo Fayose, Gwamnan jihar Benuwai ya ce ‘dan takaran shugaban kasan ya saba alkawari
  • Mukarraban Ifeanyi Okowa sun kare Atiku, sun ce shi yake da hurumin daukar abokin takararsa

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom yana zargin ‘dan takaran shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da kin bin shawarar jam’iyya.

Mai girma Samuel Ortom ya tuhumi Atiku Abubakar da laifin kin tafiya da Nyesom Wike da kuma wasu wadanda ba ayi masu adalci a jam’iyya ba.

Ayo Fayose ya na da irin wannan ra’ayi, amma rahoton Punch ya nuna ana maida masu martani daga bangaren Atiku Abubakar da Ifenayi Okowa.

Na kusa da Ifeanyi Okowa da mutanen Nyesom Wike sun tofa albarkacin bakinsu bayan kalaman da Ortom da Fayose suka yi a game da zaben 2023.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga tsaka mai-wuya a 2023, Fayose ya ce har abada Wike ba zai goyi bayansa ba

Wasu hadimai da mukarraban Gwamna Okowa da suka tattauna da Punch sun bayyana cewa yanzu abin da ke gaban PDP shi ne yadda za a ci zabe.

Zaben Gwamnan Ekiti

A zaben Ekiti, PDP ta tsaida Bisi Kolawole a matsayin ‘dan takarar Gwamna, amma ba a ga Atiku Abubakar da shugaban jam’iyya su na yi masa kamfe ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu sun zargi ‘dan takaran da kuma Iyorchia Ayu da cewa su na da hannu wajen rashin nasarar da jam’iyyar ta samu, a karshe ta zo ta uku a zaben jihar.

Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba ya ce rashin kudi ya hana jam’iyyar zuwa Ekiti domin ta tallata ‘dan takararta da kyau a zaben 2022.

Atiku, Ayu da Okowa
Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa Hoto: @IAOkowa
Asali: Twitter

An maidawa Ortom raddi

An ji Ortom yana cewa ya kamata Atiku Abubakar ya sasanta da Gwamna Nyesom Wike tun wuri.

Kara karanta wannan

Wani shahararren gwamnan PDP: Har yanzu Allah bai yarje min na goyi bayan Atiku ba

Amma wata majiya daga jam’iyyar PDP ta soki Gwamnan na Benuwai, ta ce Wike ya tattara ya bar Najeriya zuwa kasar waje kafin mutanen Atiku su neme shi.

A cewar wannan mutumi wanda babba ne a jam’iyya, ba Gwamna Wike kadai aka fusata a PDP ba, yake cewa babu dalilin yin garaje wajen sulhun da za ayi.

Hon. Nwuke ya kare Wike

Tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Ogbonna Nwuke ya goyi bayan Ortom, yake cewa ba ayi wa Wike adalci bayan zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa ba.

Amma sakataren yada labarai na Gwamnan Delta, Olisa Ifeajika ya sha bam-bam, ya na mai cewa Atiku Abubakar ne yake da hurumin zaben abokin takararsa.

Ifeajika ya yi kira ga Gwamnan na Benuwai da sauran ire-irensa da su goyi bayan Atiku da Okowa

Martanin Atiku Abubakar

Mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar, Paul Ibe ya ce jam’iyya za ta cigaba da lallashin duk wadanda suke ganin ba ayi masu adalci a tafiyar ta 2023 ba.

Kara karanta wannan

Takardun makarantar da Atiku, Tinubu, Kwankwaso da Obi suka gabatarwa hukumar INEC

An rahoto Paul Ibe yana cewa ana samun sabani a siyasa, ya ce babban kalubalen da ke gaban PDP shi ne yadda za a ci zabe, a karbe mulki daga hannun APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel