Mutanen Tinubu sun fara zawarcin jam’iyyun da basu da yan takarar shugaban kasa

Mutanen Tinubu sun fara zawarcin jam’iyyun da basu da yan takarar shugaban kasa

  • Gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, dan takarar jam’iyyar APC, Bola Tinubu na kara samun karfi a kasar Yarbawa
  • A yanzu haka, gamayyar kungiyoyin kudu maso yamma masu goyon bayan Ajandar Tinubu a 2023 sun fara zawarcin wasu kananan jam’iyyun siyasa
  • Hakazalika suna kokarin ganin sun shawo kan fusatattun mambobin APC da suka koma wasu jam’iyyun domin ganin sun marawa Tinubun baya a zaben

Oyo - Kungiyoyin kamfen din dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, sun fara tattaunawa da kulla yarjejeniya da sauran jam’iyyun siyasa da basu da yan takarar shugaban kasa, jaridar Punch ta rahoto.

An tattaro cewa kungiyoyin wadanda ke kudu maso yamma amma suna da wakilai a sauran yankunan kasar, suna duba yiwuwar kulla kawance da sauran jam’iyyu don ganin sun marawa takarar Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023

Bola Tinubu
Mutanen Tinubu sun fara zawarcin jam’iyyun da basu da yan takarar shugaban kasa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban wannan tafiya ta ‘South-West Agenda for Asiwaju 2023’ na kasa, Sanata Adesoji Akanbi, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai.

Akanbi, wanda ya hada kungiyar ta goyon bayan Bola Ahmed Tinubu wacce ke da zama a jihar Oyo ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Abun da muke kokarin yi a wannan gamayyar kungiya shine cewa mutane da dama suna fushi da jam’iyyunsu, watakila saboda zabukan fidda gwani masu cike da zamba, sannan suka koma wasu jam’iyyun. Muna kokarin samun irin wadannan mutane a hannu, ba wai jam’iyyu kawai ba.”

Da aka tambaye shi game da wadanda suka fusata a APC, sai ya ce:

“Sune ma ainahin wadanda muke son samu. Sun bar APC watakila saboda gwamnoninsu ne suka haddasa haka. Muna kokarin lallashinsu kada su yi takarar kowace kujera a wata jam’iyyar amma su yi aiki tare da mu; su marawa Bola Ahmed Tinubu baya.

Kara karanta wannan

Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili

“Ba wai muna cewa su marawa dukkanin yan takarar APC baya bane saboda a yanzu suna wasu jam’iyyun. Maimakon su yi asarar kuri’unsu da kokarinsu a kan yan takarar shugaban kasa na sabbin jam’iyyunsu wadanda basu da alaka da su a baya, mai zai hana su yi aiki tare da mu?"

Akanbi ya bayyana cewa koda dai ba dukkanin jam’iyyun siyasa 18 da suka yi rijista da Hukumar zabe bane suka cike yan takarar shugaban kasa.

“Hatta ga wadanda suka cike yan takara, reshen jihohin wasun su basa la’akari da yan takarar saboda jam’iyyun basu da isassun kudaden kula da su. Don haka, suna iya aiki tare da mu, duba ga cewar Asiwaju zai yaba masu idan ya lashe zaben.”

Ingiza mai kantu: Kungiyar Yarbawa ta zargi Arewa da kullawa Tinubu tuggu a zaben shugaban kasa na 2023

A wani labarin, wata kungiyar zamantakewa da siyasa ta kudu maso yammacin kasar, wacce aka fi sani da Igbimo Apapo Yoruba Lagbaye, ta yi zargin cewa ana kulla-kulla son fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC daga tseren kujerar a 2023.

Kara karanta wannan

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

Kungiyar ta bayyana cewa wasu yan siyasar arewa sun kammala shiri tsaf don tabbatar da ganin cewa Tinubu ya fita daga takarar shugaban kasa na 2023, jaridar Vanguard ta rahoto.

A wani taron da suka gudanar a Abuja, shugaban kungiyar, Aare Omoluabi Oladotun Hassan, ya ce kungiyar na da bayanai abun dogaro kan kulla-kullan na son maimaita abun da aka yiwa Obafemi Awolowo da MKO Abiola don ganin Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar PDP ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel