Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili

Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili

  • An yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da kada su barnatar da kuri’unsu wajen zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar
  • Wakiliyar jihar Enugu a hukumar da'a ta tarayya Amb Ginika Tor ne ta yi wannan kiran a wani rahoto
  • Ta kuma bukaci da a bar dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya lashe zabe daga shiyyar

Amb Ginika Tor ta yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da kada su yi kuskuren zaben jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Wakiliyar ta jihar Enugu a hukumar da’a ta tarayya ta ce jam’iyyar PDP ba ta cancanci kuri’un kabilun Igbo ba, saboda kin amincewar jam’iyyar na ba da tikitin takarar shugaban kasa a yankin kudu maso gabas, inji rahoton jaridar The Nation.

'Yar siyasa ta bayyana dalilin da zai sa Tinubu ya samu karbuwa a yankin Ibo
Jigon siyasa: Dalilin da ya sa Igbo za su kadawa Tinubu kuri’a a 2023 | Hoto: today.ng
Asali: UGC

Ta ce a maimakon goyon bayan Atiku tare da kada masa kuri'u, ya kamata dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shahara ya kuma mamaye kuri'un yankin.

A cewarta, Tinubu ne kadai dan takarar da ke da karfin kare muradun al’ummar yankin Kudu maso Gabas, idan aka duba tarihinsa a matsayinsa na dan Najeriya da bai nuna bambancin kabila.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Today ta naqalto ta tana cewa:

“Muna kuma taya dan takarar shugaban kasa a yau, Bola Ahmed Tinubu na babbar jam’iyyar mu ta APC murna.
“Muna goyon bayan shugaban mu mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, saboda irin nasarorin da ya samu. Shi maginin jama'a ne.
“Duk inda na je, kididdigar da na samu, duk abin da kuke ji shi ne ya tsufa. Babu wanda ya ce bai cimma wani abu mai ma'ana ga al'umma ba.

“Amma akwai abin da ba za ka iya kwacewa daga hannun Bola Ahmed Tinubu ba, yana da tasiri a idon mutane, yana gina mutane kuma ina goyon bayansa ta hanyar karfafa mutane, domin Allah Ya sa na zama muryar marasa murya."

Jigon siyasa: Cikin APC da PDP ya duri ruwa ganin yadda Peter Obi ya samu karbuwa

A wani labarin, Sanata Victor Umeh ya bayyana cewa gungun jama’a da ke kaunar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi, ya zama abin damuwa ga jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa, PDP.

Jaridar Punch ta rahoto cewa Umeh ya bayyana hakan ne a wani sashe na tattaunawa da wasu ‘yan kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, a Awka, babban birnin jihar Anambra a ranar Talata, 21 ga watan Yuni.

Yace: “Goyon bayan da ‘yan Najeriya ke baiwa tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, yana ba ‘ya’yan jam’iyyar APC, PDP, da sauran jam’iyyu tsoro sosai gabanin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel